Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da shugabar kasar Namibia Netumbo Nandi-Ndaitwah a nan birnin Beijing. Yayin ganawar shugabannin biyu a yau Juma’a, sun fitar da sanarwar hadin gwiwa mai kunshe da aniyarsu, ta daga matsayin alakar kasashen biyu zuwa dangantakar al’ummun Sin da Namibia mai makomar bai daya a sabon zamani.
Kazalika, shugaba Xi ya ce JKS na jagorantar daukacin al’ummun sassan kasarsa, wajen cimma cikakkiyar nasarar farfado da kasa bisa salon zamanantarwa irin na Sin.
A gabar da ita ma Namibia ke yunkurawa don cimma kudurorin ci gabanta na dogon lokaci nan zuwa shekarar 2030, kuma hakan ya dace da lokacin da ake ciki, da zarafi na zurfafa hadin gwiwar kawance tsakanin kasashen biyu. (Saminu Alhassan)














