ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur

by Abubakar Sulaiman and Idris Aliyu Daudawa
2 hours ago
Mai

Duk da yake akwai maganar faɗuwar farashin manfetur wannan kuma ya biyo bayana ɗan tsagaita wutar da aka yi, hakan shi ya kawo faɗuwar farashin  ɗanyen mai bayan da aka shiga halin zaman ɗar ɗar ya kwanta saboda tsagaita wuta  agabas ta tsakiya, har yanzu farashin manfetur Naira N1, 24, a tashoshin mai a faɗin tarayyar Nijeriya.

Jaridar Blueprint ta ƙarshen mako za ta iya tunawa a shekarun baya ana sayar da farashin manfetur ne Naira 770 ko Naira 800 kafin yaƙin Iran, yanzu ana sayar da shi ne tsakanin Naira 1, 200 ko Naira 1, 300 kowace lita wannan kuma ya danganta ne da wurin da mutum ya ke.

Maganar kiraye- kirayen da ake yi akan rage farashin ɗanyen mai ta ƙaru ne a makonnin da suka gabata saboda kuwa lokacin da ake ta fafata yaƙi sosai tsakanin Amurka da Iran ana sayar litar ɗanyen mai ɗaya dala 114 zuwa dala kusa da 71 na kowace gangar ɗanyen man, wannan kuwa ya biyo bayan tsagaita wutar da aka yi tsakanin Iran da Isra’iala, wannan kuma ya biyo bayan buɗe mashigin jiragen ruwa da suke bi ta hanyar ta Hormuz.

ADVERTISEMENT

Sanadiyar hakan ne ta sa ƙaramin Ministan albarkatun manfetur, da Heineken Lokpobiri, da hukumar kare hakkin masu amfani da kaya, ta tsaya kai da fata cewa ya dace a rage farashin  na manfetur tare da la’akari da yadda farashin  manfetur a  kasuwannin mai na duniya.

Nuna rashin jin daɗin lamarin

LABARAI MASU NASABA

2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa

An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa

Wani mai jimirin shiga motar haya, Amaka Aslem, wanda kuma shi ma’aikaci ne, ya nuna rashin jin daɗin sa dangane da ƙaruwar farashin, wanda har ma abin ya ba shi mamaki inda ya ke cewa shi bai ga wani dalilin da zai sa ƴan Nijeriya za su riƙa sayen litar mai ɗaya fiye da tsakanin Naira N1,200 zuwa N1,300?

“Lokacin da aka shiga cikin halin ƙaƙa-nika-yi wurin mashigin ruwan na Hormuz lokacin da jiragen ruwa masu dakon ɗanyen manfetur, ba a basu dama ce ta wucewa ba domin kai ɗanyen man zuwa wasu ƙasashe ba, saboda halin yaƙin da ake ciki a lokacin tsakanin Amerika Isra’ila da Iran ai nan da nan ne sai farashin mai ya tashi fiye da tunanin kowa. Yanzu da aka samu dama yanayin ya sauya tunda har farashin ɗanyen mai ya faɗi me kuma ya sa ake ɗaukar lokaci  har zuwa yanzu su Talakawa ba’a sakar masu mara ba, su san cewa su ma ƴan Adam ne a rage kuɗin na manfetur?

“Lamari da akwai mamaki ƙwarai da gaske domin kuwa yadda ake saurin ƙara farashin bai yi daidai da jinkiri na ƙin son rage shi ba.Me yasa muke yiwa kan mu haka?  Ga shi mun yi sa’a muna daga ƙasa ne wadda ta ke da man da albarkatun shi amma sai ga shi muna ta kururuwar a rage mana farashin manfetur kamar yadda ta ce cikin tambayar da ta yi,”.

Shi ma wani mai mota, Isah Jatau, cewa ya yi har abin ya ɗaure ma shi kai ta yadda masu harkokin da ke zaman kansu suke ci gaba da sayar da manfetur fiye da Naira 1, 300 kowace litar manfetur duk kuwa da ya ke akwai ci gaban da aka samu a kasuwar mai ta ƙasa da ƙasa.

Ya ce,“Nijeriya a matsayin ta na ƙasa wadda take samar da ɗanyen manfetur,ya kamata ta san duk hanya ko hanyoyin da za ta bi domin ta kare mutanen ƙasar ta daga irin halin da za su shiga kan lamarin  ko halin da suka tsinci kansu duk lokacin da aka yi ƙarin farashin kuɗin manfetur  wato kamar yadda shi ɗanyen man farashin shi ya ke hawa da sauka.Ya ƙara da cewa duk lokacin da farashin ɗanyen manfetur ya tashi  a kasuwar mmai ta duniya masu harkar manfetur nan da nan ba tare da ɓata lokaci ba, su ke ƙara farashin na mai, sai dai kuma  wani abu mai ɗaure kai duk lokacin da, farashin na ɗanyen man  ya faɗi ko sauka sai su zama ba su son  rage farashin man na su.”

Hakanan ma direban motar  fasinja da ake kira Bolt ya yi da masu shigo da Fetur daga waje, cewa ya yi su yi koyi wajen amfani da yadda farashin man yake a ƙasashen waje manufa anan ita ce yadda farashin ɗanyen man ya ke.

“Faɗuwar farashin ɗanyen man da bata daɗe ba ta samar da wata dama ce ta yadda su masu tuƙa mota mu samu sauƙi ta yadda suma waɗanda muke mu’amalar da su, su ma su amfana. Amma farashin man a yanzu ya shafi harkokin mu ba kuma da ƙaramin tasiri ya yi ba. Domin kuwa mun samu raguwa masu shiga motar saboda ba za su iya biyan kuɗin da muka ƙara baa bin sai dai haƙuri kawai kamar yadda ya nuna damuwar sa kan lamarin,”.

Yadda lamarin ya ke a ƙasashen duniya

Sai dai kuma kamar yadda ya ke bayyana dalilan da suka farashin mai bai samu komawa kamar yadda ya ke a baya ba,wani masanin ci gaban tattalin arziki, Dakta. Emeka Duruoha, cewa ya yi lamarin ba Nijeriya kaɗai ya shafa ba,abin ya shafi duniya ne gaba ɗaya.

Ya ce muddin dai waɗanda suke da ruwa da tsaki basu daina yin duk waɗansu abubuwan da za su iya tada hankali ba, bayan sun riga sun sa hannu kan lamarin zaman lafiya wato ya kasance sun yi biris da lamarin to babu wani abinda zai canza.

Ya ƙara jaddada cewa masu ruwa da tsaki a harkar da ta shafi manfetur waɗanda kuma suna amfana daga dukkan abubuwan da suke faruwa ta waccan hanya ko kuma wannan, su suna buƙatar ne su ci gaba da amfana da abubuwan da suke, saboda su ƙara samarwa kansu riba.

“Da farko kamar yadda ya ce ya kamata, mu san yadda yadda kasuwar ko harkar mai ta ke yin aiki. Na fahimci cewar wannan lamari ne da ya shafi duniya gaba ɗaya. Ko ma Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump sai da ya kafa wata hukuma da ta sa dole ne sai an sake duba farashin na albarkatun manfetur a Amirka. Ko da a ƙasar Amirka ma, farashin bai dawo ƙasa ba kamar yadda ake son ko tsammani.

“Ba za a iya jin labarin da an sake duba shi lamarin da ya ke da alaƙa da zarar an ƙaara kuɗin manfetur da nau’oin sa wato albarkatun shi bada daɗewar ƙarin ba.Wani abu ne na taka – tsantsan kuma  hankali ake yin shi, dole kuma ana tuna da cewa idan an samu wani sabon abu game da farashin ɗanyan mai, a yanayin da ake ciki, watakila abin da ya shafi ƙarin ya fara yau, gobe,ko kuma Jibi, za a fara ganin ƙarin ko ragin ya fara aiki nan take ba, lamarin da ya shafi hakan abin bai kasancewa hakanan kawa ba.

“Ya kuma kamata a tuna da cewa masu harkar kasuwanci maza da mata suna yin hakan ne doimin su samu daidai ribar da suke so. Abinda ya kamata  a sani shi ne idan da akwai ƙarin farashin mai a yau, nan da nan za a fara aiki d yin hakan  aranar ba tare da ɓata lokaci ba. Amma idan  farashin ne ake buƙatar ragewa ,abin yana ɗaukar lokaci mai tsawo kafin a samu rage shi farashini. Wannan kuma saboda maganar gaskiya ƴan kasuwa su buƙatar su ita ce su samu babbar riba.

Abin da masana suka ce 

Wani masanin tattalin arzikin da ya sahfi manfetur wanda kuma tsohon mamba ne na ƙungiyar masana tattalin arziki ne (NES), Dakta. Chuchs Iguebe, cewa masu amfani da abu dama ko tuni aka san su da buƙatar kuma suna da nasu dalilin, na buƙatar samun farashin manfetur mafi sauƙi musamman ma idan aka yi la’akari da yadda farashin ɗanyen mai ya faɗi a kasuwar mai ta duniya.

Cewa ya yi, “Maganar neman farashin mafi sauƙi hakan ba wani laifi bane. Idan aka duba yadda aka samu raguwar farashi na ɗanyen man, kamata ya yi yadda yanayin farashin yake abin ya yi bankwana daga mai tsada, kamar dai yadda abin yake a ƙasar Amurka kafain a kai ga sa hannu a yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran.”

A na shi jawabin, babban jami’i na AGIk Consultancies, wata kamar ƙungiya ko hukuma wadda da ƙware kan harkokin da suka shafi kuɗi, Mista. Ademola Adigun, cewa ya yi shi lamarin dawo da farashin albarkatun manfetur hakan yana ɗaukar makonni kafin a kai ga ɗaukar mataki na yin gyara, amma ba cikin ɗan ƙaramin lokaci ba.

Mai
Abubakar Sulaiman
Website |  + posts Bio
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Daƙile Harin Ƴan Bindiga A Wani Ƙauyen Katsina
  • Abubakar Sulaiman
    Yadda Jana’izar Ruhullah Khomeini Ta Shiga Kundin Tarihi Na Guinness
  • Abubakar Sulaiman
    NIMC Ta Yi Haɗin Gwuiwa Da Ma’aikatun Gwamnati Don Faɗaɗa Rajistar NIN
  • Abubakar Sulaiman
    Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisar Kan Gyaran Kudirin Dokar Shari’ar Manyan Laifuka
Mai
Idris Aliyu Daudawa
+ posts Bio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Yajin Aiki: Ƙungiyar Likitocin Nijeriya Ta Ba Gwamnati Wa’adin Mako Huɗu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Ba Mu Yarda Da Maƙiyanmu Ba, A Shirye Muke —Iran
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Yadda Jihohi Suka Fara Ɗanɗana Ambaliyar Ruwa A Daminar Bana
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    ‘Lokaci Ya Yi Na Ɗaukar Mataki Kan Masu Yanke Hukunci Da Kansu’

MASU ALAKA

2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa
Da ɗumi-ɗuminsa

2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa

July 10, 2026
An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa
Manyan Labarai

An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa

July 10, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Manyan Labarai

Sana’ar Ɗinki: Yadda Telolin Zariya Suka Yi Fice A Sassan Afirka

July 10, 2026
Next Post
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Ɗantsoho Ya Jinjina Wa Hukumar FCC Kan Sabbin Sauye-Sauyen Da Ta Samar

LABARAI MASU NASABA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Ɗantsoho Ya Jinjina Wa Hukumar FCC Kan Sabbin Sauye-Sauyen Da Ta Samar

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur

July 11, 2026
Kasar Sin Ta Fitar Da Shirin Kai Wa Matakin Koli Na Fitar Da Hayakin Carbon

Kasar Sin Ta Fitar Da Shirin Kai Wa Matakin Koli Na Fitar Da Hayakin Carbon

July 10, 2026
Sin Ta Yi Nasarar Dawo Da Rokar Da Ake Sarrafa Dawowarta A Tashin Farko Na Samfurin Long March-10B

Sin Ta Yi Nasarar Dawo Da Rokar Da Ake Sarrafa Dawowarta A Tashin Farko Na Samfurin Long March-10B

July 10, 2026
CMG Ya Gabatar Da Shiri Na Musamman Mai Taken “Samun Nasara Dangane Da AI+” A Ketare

CMG Ya Gabatar Da Shiri Na Musamman Mai Taken “Samun Nasara Dangane Da AI+” A Ketare

July 10, 2026
Zargin Da Wasu Sassa Ke Yiwa Kasar Sin Na Takure Sauran Kasashe Masu Tasowa Ba Shi da Tushe Ko Makama

Zargin Da Wasu Sassa Ke Yiwa Kasar Sin Na Takure Sauran Kasashe Masu Tasowa Ba Shi da Tushe Ko Makama

July 10, 2026
2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa

2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa

July 10, 2026
Taron Kara Wa Juna Sani Na Duniya Ya Yi Nazari Kan Kwarewar Kasar Sin Wajen Rage Talauci

Taron Kara Wa Juna Sani Na Duniya Ya Yi Nazari Kan Kwarewar Kasar Sin Wajen Rage Talauci

July 10, 2026
An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa

An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa

July 10, 2026
Xi Ya Zanta Da Shugabar Namibia

Xi Ya Zanta Da Shugabar Namibia

July 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.