ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shin Har Yanzu Shettima Ne Abokin Takarar Tinubu?

by Sulaiman
3 months ago
Tinubu

Duk da wasu alamu a baya sun nuna cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu zai maye gurbin mataimakinsa, Kashim Shettima, saboda dalilan siyasa da wasu dalilai na musamman ga Nijeriya, ana ganin wannan tunanin ya gushe.

Ba da jimawa ba ‘yan Nijeriya za su san gaskiyar lamarin idan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bude shafinta don jam’iyyun siyasa su mika jerin ‘yan takararsu na dukkan mukaman zabe.

Haka kuma idan INEC ta fitar da jerin sunayen ‘yan takara na kowanne jam’iyya, za a iya samun abin mamaki. Za a iya samun wasu sunaye da ba a baba zata ba a matsayin ‘yan takara, wanda na iya kawo rikici a wasu jam’iyyun.

ADVERTISEMENT

A halin yanzu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ne ya bayyana wanda zai yi masa mataimaki.A cikin jam’iyya mai mulki ta APC, fadar shugaban kasa tun da dadewa ta umurci ministoci da ma’aikata na musamman su yi gum game da yiwuwar sauyi a tikitin 2027 bayan gargadi na farko ga mambobin majalisar ministoci.

Dokar kame baki na iya kasancewa har yanzu saboda shugaban kasa bai bayyana Shettima a fili a matsayin abokin takararsa ba.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Akwai rahotannin da suka nuna cewa a karshen shekarar da ta gabata, Rabiu Kwankwaso, wanda yanzu shi ne abokin takarar Obi, ya shafe shekaru biyu da rabi na farkon gwamnatin Tinubu yana tattaunawa don maye gurbin Shettima a 2027. Har sai da Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf ya balle daga karkashin Kwankwaso.

Amma alamar da ta fi bayyana cewa muhawarar tattaunawar abokin takara na iya karewa, saboda shugaban kasa ya zabi Shettima wajen tsayawa takarar shugabancin kasa a 2027 a karkashin tutar jam’iyyar APC tun kafin ya lashe zaben fid da gwani.

Sai kuma kalamun da Shettima ya yi, bayan zaben fitar da gwani, kan wasu ‘yan’uwa da ba a ambata sunayensu ba wadanda ake cewa sun gaya wa Tinubu ka da ya saka tufafin da Shettima ya ba shi saboda ana iya kumuwa da wata irin guba.

Shawarar na nufin so ake a cire Shettima daga matsayin mataimakin shugaban kasa. A fili yake cewa mataimakin shugaban kasa ya tabbatar da cewa matsayinsa a APC a yanzu ya baya fuskantar barazana. Watakila haka ne ko kuma ba haka ba.

Shugaba Tinubu shi kansa sau da yawa ya yi kokarin zama mataimakin shugaban kasa a cikin shekaru 20 da suka gabata.kokarin farko nasa ya kasance a shekarar 2007. Ya sake kokari a shekarar 2011, inda ya fito da wata dabara a karshe lokacin da jam’iyyun siyasa za su iya maye gurbin ‘yan takara kafin a rufe. Ya sa Tunde Bakare ya yi murabus bayan zaben. Bakare shi ne mataimakin Muhammadu Buhari a karkashin jam’iyyar CPC.

Don haka, a bangaren shugaban kasa, maye gurbin daya daga cikin ‘yan takara da wani don karfafa takara ko daidaita yanayin shagabanci ba wani sabon abu ba ne. Ya taba yin hakan a Legas. Lokacin da Buhari da Tinubu suka cimma matsaya, shekaru hudu sun shude.Kuma a wannan karon, tsarin zaben mataimakin takara shi ne mafi rikici da aka taba samu a Nijeriya.

Sai dai idan Tinubu ya dauki shekarar 2027 a matsayin wata dama don sake tsara daidaiton iko tsakanin arewa da kudu, tsakanin addinai da kuma tsarin zamantakewa da siyasa da ake da shi.

Tinubu
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar
  • Sulaiman
    Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030
  • Sulaiman
    Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari
  • Sulaiman
    Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

MASU ALAKA

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026  Mrs Zubaida Umar
Labarai

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

September 11, 2026
Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro
Manyan Labarai

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 11, 2026
Sanata yari
Labarai

Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari

September 11, 2026
Next Post
Ɗan Kwankwaso Ya Zama Mataimakin Ɗan Takarar Gwamnan NDC A Zaɓen Kano na 2027

SAW

Ɗabi’un Annabi (SAW) Kan Abubuwa Na Al’adar Rayuwa

September 11, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000

Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000

September 11, 2026
Tinubu

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

September 11, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.