ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gabas Ta Tsakiya: Ya Wajaba A Aiwatar Da Matakan Kawo Karshen Yaki Ba Wai Takaita Wuta Na Dan Lokaci Ba

by CGTN Hausa and Sulaiman
5 months ago
Gabas

Sanarwar baya bayan nan ta tsagaita bude wuta mai wa’adin makonni biyu tsakanin Amurka da Iran wadda kuma Israila ta goyi baya, ta faranta ran sassan kasa da kasa, ko da yake hakan ba ya nuni ga kawo karshen yankin baki daya. Illa dai mataki ne mai matukar muhimmanci na sassauta mummunan yanayin da aka shiga.

Al’ummun duniya sun shaida makonni na dauki ba dadi, da tattaunawar bayan fage tsakanin wasu sassa, da matsin lamba daga sassan kasa da kasa, bayan tafka asarar rayuka da lalata tarin ababen more rayuwa. Kazalika, an ga yadda kasuwar albarkatun mai ta shiga wani hali na matsi, bayan katsewar hanyar sufurin danyen mai ta mashigin Hormuz, wanda hakan ya yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya baki daya.

A takaice, dukkanin kasashen duniya sun dandana mummunan tasirin wannan yaki, sun kuma kara fahimtar muhimmancin kaucewa ci gabansa, da ma matukar bukatar kawo karshensa baki daya.

ADVERTISEMENT

Masharhanta da dama na cewa, tun asali ma bai kamata a tsunduma cikin wannan yaki ba, wato dai kasashen da suka jawo barkewarsa sun zabi yin hakan ne bisa radin kansu, ba wai domin ya zama wajibi ba. Kuma ba su yi la’akari da muradun sauran kasashen duniya ba. Hakan ne ma ya sa kasashen da suka shige gaba, wajen ganin an cimma matsayar tsagaita wutar yakin, kamar Sin da Pakistan da suka gabatar da shawarwarin cimma wannan buri, suka sha nanata haramcin kaddamar da yaki ba tare da amincewar kwamitin tsaron MDD ba.

Muna iya cewa wannan mataki na dakatar da bude wuta na makonni biyu, wata dama ce aka samu ta komawa ga diflomasiyya. To sai dai kuma akwai masu ganin cewa da wuya Iran ta saki jiki da matakin, duba da cewa a baya ana tsaka da tattaunawa ne aka fara kaddamar da hare-hare kan yankunanta. Hakan ya sa matakan da za mu gani a yanzu ke da matukar muhimmanci, wajen tabbatar da ko dakatar da bude wutar zai haifar da matakan din din din na kawo karshen yakin ko kuwa a’a.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Amma a bangaren akasarin kasashen duniya masu fatan ganin an kawo karshen wannan yaki baki daya, burinsu shi ne tsagaita wutar na yanzu ya kai ga samar da dama ta cimma cikakkiyar yarjejeniya. Sassan kasa da kasa na da burin ganin bayan wannan yaki baki daya, tare da fatan hana maimaituwarsa a nan gaba. (Saminu Alhassan)

Gabas
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Gabas
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

September 8, 2026

Next Post
Gwamnatin Bauchi Ta Rufe Kasuwannin Shanu 25 Saboda Matsalar Tsaro

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci