ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 16, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gargaɗi: ‘Yansanda Sun Gano Shirin Kai Hare-hare A Makarantu Da Wuraren Ibada

by Sulaiman
22 hours ago
'yansanda

Rundunar ‘Yansandan Nijeriya ta fitar da gargadin tsaro a faɗin ƙasar kan yiwuwar kai hare-haren ta’addanci a makarantu, wuraren ibada, sansanonin horas da matasa na NYSC da sauran wuraren tarukan al’umma.

Gargadin ya biyo bayan bayanan sirri da suka nuna cewa wasu ‘yan ta’adda na shirin gudanar da hare-hare a sassa daban-daban na ƙasar, musamman yankunan Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma, Arewa ta Tsakiya da wasu sassan Kudu maso Yamma.

Rundunar ta kuma bayyana damuwa kan rahotannin motsin wasu ‘yan bindiga dauke da makamai daga Katsina ta Kaduna zuwa Jihar Filato, yayin da ake zargin wasu ‘yan ISWAP da masu haɗin gwiwarsu na gudanar da sa ido kan wuraren da za su iya kai hari.

ADVERTISEMENT

‘Yansandan sun ce makarantu na cikin wuraren da suka fi fuskantar barazana, musamman yayin da ake shirin komawa karatu a zangon shekarar 2026/2027, inda ‘yan ta’adda za su iya amfani da cunkoson ɗalibai da malamai wajen haddasa asarar rayuka masu yawa.

Bayanin sirrin ya kuma nuna yiwuwar kai hare-hare gabanin babban zaɓen 2027, da nufin haifar da tsoro da dagula zaman lafiyar al’umma.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnan Kano Ya Naɗa Hafsat Kutama Mukaddashiyar Shugabar Hukumar PCACC 

TCN Ta Samar Da Hanyar Samun Wutar Lantarki A Kebbi Ta Wucin Gadi

Saboda haka, Rundunar ta umarci kwamandojin ‘yansanda da su ƙara sa ido da sintiri, binciken ababen hawa da mutane, tare da tsaurara matakan tsaro a makarantu, wuraren ibada, sansanonin NYSC da sauran wurare masu muhimmanci.

Ta kuma bukaci a ƙarfafa jami’an kai agajin gaggawa tare da tsaurara tsaro a kan iyakokin jihohi, hanyoyin shiga da fita da sauran muhimman hanyoyin da ‘yan ta’adda za su iya amfani da su.

Yansanda
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwamnan Kano Ya Naɗa Hafsat Kutama Mukaddashiyar Shugabar Hukumar PCACC 
  • Sulaiman
    Rokar Gravity-1 Na Kasar Sin Ya Harba Sabbin Taurarin Dan’adam Daga Teku
  • Sulaiman
    An Bude Taron Kasa Da Kasa Karo Na 5 Dangane Da Tsarin Cin Gajiyar Fasahar Taurarin Dan Adam Na Beidou
  • Sulaiman
    Sin Ta Yi Nasarar Harba Taurarin Dan Adam 10 Ta Amfani Da Rokar Zhuque-2E

MASU ALAKA

Gwamnan Kano Ya Naɗa Hafsat Kutama Mukaddashiyar Shugabar Hukumar PCACC 
Manyan Labarai

Gwamnan Kano Ya Naɗa Hafsat Kutama Mukaddashiyar Shugabar Hukumar PCACC 

September 16, 2026
TCN Ta Samar Da Hanyar Samun Wutar Lantarki A Kebbi Ta Wucin Gadi
Labarai

TCN Ta Samar Da Hanyar Samun Wutar Lantarki A Kebbi Ta Wucin Gadi

September 16, 2026
APC Ta Tsawaita Rijistar Mambobinta, Ta Ɗage Ranar Babban Taronta Na Ƙasa
Labarai

APC Ta Nemi A Gudanar Da Bincike Kan Farmakin Da A Kai Ofisoshinta A Kaduna

September 16, 2026
Next Post
Sin Ta Yi Kira Da Zurfafa Hadin Kai A Babban Taron IAEA

Sin Ta Yi Kira Da Zurfafa Hadin Kai A Babban Taron IAEA

LABARAI MASU NASABA

Gwamnan Kano Ya Naɗa Hafsat Kutama Mukaddashiyar Shugabar Hukumar PCACC 

Gwamnan Kano Ya Naɗa Hafsat Kutama Mukaddashiyar Shugabar Hukumar PCACC 

September 16, 2026
Rokar Gravity-1 Na Kasar Sin Ya Harba Sabbin Taurarin Dan’adam Daga Teku

Rokar Gravity-1 Na Kasar Sin Ya Harba Sabbin Taurarin Dan’adam Daga Teku

September 16, 2026
TCN Ta Samar Da Hanyar Samun Wutar Lantarki A Kebbi Ta Wucin Gadi

TCN Ta Samar Da Hanyar Samun Wutar Lantarki A Kebbi Ta Wucin Gadi

September 16, 2026
APC Ta Tsawaita Rijistar Mambobinta, Ta Ɗage Ranar Babban Taronta Na Ƙasa

APC Ta Nemi A Gudanar Da Bincike Kan Farmakin Da A Kai Ofisoshinta A Kaduna

September 16, 2026
2023: Me Ya Sa Ake Rububin Wike?

Ban Taɓa Yi Wa Tinubu Alƙawarin Zan Koma APC Ba – Wike

September 16, 2026
Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda Sama Da 1,100 Cikin Shekara Ɗaya – Kwamanda

Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda Sama Da 1,100 Cikin Shekara Ɗaya – Kwamanda

September 16, 2026
Tinubu Zai Kayar Da Atiku Da Obi Ko Da Sun Haɗa Kai – Fayose

Tinubu Zai Kayar Da Atiku Da Obi Ko Da Sun Haɗa Kai – Fayose

September 16, 2026
Jarumin Nollywood Olu Jacobs Ya Rasu Yana Da Shekaru 84

Jarumin Nollywood Olu Jacobs Ya Rasu Yana Da Shekaru 84

September 16, 2026
Sojoji Sun Ceto Mutane 10 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

Sojoji Sun Ceto Mutane 10 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

September 16, 2026
Nan Gaba TIinubu A Wajen Opay Da Moniepoint Zai Nemi Rancen Kuɗi – Dino Melaye

Gwamnati Ba Ta Da Hurumin Ɗaukar Nauyin Yi Wa Mutane Aure – Dino Melaye

September 16, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.