ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Lawal Ya Kafa Tarihi, Yayin Da Aka Fara Jigilar Alhazai Daga Filin Jirgin Sama Na Gusau

by Sulaiman
4 months ago
Lawal

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kafa sabon tarihi bayan da aka gudanar da jigilar farko na aikin Hajji daga Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa da ke Gusau.

Jirgin Hajjin na farko ya tashi ne daga filin jirgin ranar Juma’a ɗauke da maniyyata 415 na jihar Zamfara a jirgin kamfanin Max Air mai lamba NGL270 zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana.

Rahotanni sun nuna cewa daga cikin maniyyatan akwai maza 288 da mata 127.Da yake jawabi yayin ƙaddamar da tashin jirgin, Gwamna Lawal ya bayyana farin cikin sa da godiyar sa bisa ganin wannan gagarumin ci gaba da ya ce zai kasance abin tarihi a jihar Zamfara.Gwamnan ya bayyana gina Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Gusau a matsayin ɗaya daga cikin manyan ayyukan tarihi da gwamnatin sa ta sa a gaba, kuma alhamdu lillahi, ta cimma nasara.

ADVERTISEMENT

“Ina farin ciki matuƙa a yau ganin maniyyatan mu suna tashi kai tsaye daga Filin Jirgin Sama na Gusau zuwa ƙasar Saudiyya domin aikin Hajjin bana,” in ji gwamnan.

Ya ƙara da cewa, mutane da dama sun yi shakku kan yiwuwar aikin ya zama gaskiya, amma yanzu an tabbatar da hakan bayan an fara aikin gina filin jirgin tun ranar 18 ga watan Yunin 2024.

LABARAI MASU NASABA

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

“Ba zan iya bayyana irin farin cikin da nake ciki ba. Wannan babbar dama ce ga maniyyatanmu domin tafiya cikin sauƙi da kwanciyar hankali. Cikin ƙasa da awa huɗu za su isa Saudiyya. A baya kuwa sai sun je Kano ko Sakkwato kafin su samu jirgin Hajji,” in ji gwamnan.

Gwamnan ya ce, wannan nasara wata babban mataki ne na tarihi tare da cika ɗaya daga cikin alƙawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe.“Wannan tarihi ne mai girma kuma cikar alƙawarin da muka yi wa al’umma. Ina da ƙudurin ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaba domin jihar mu,” in ji shi.

Ya gode wa al’ummar jihar bisa addu’o’insu da kuma amincewar da suka nuna ga gwamnatinsa, yana mai cewa wannan shi ne farkon wasu manyan nasarori.Haka kuma gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta fara tattaunawa da kamfanonin jiragen sama domin fara zirga-zirgar kasuwanci daga Filin Jirgin Sama na Gusau nan gaba.

A ƙarshe, ya yi wa maniyyatan fatan sauka lafiya da gudanar da Hajji cikin nasara, tare da roƙon su da su yi addu’a ga jihar Zamfara da ma Nijeriya baki ɗaya.

Sanarwar ta fito ne ta hannun mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, SULAIMAN BALA IDRIS.

Lawal
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
  • Sulaiman
    Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

MASU ALAKA

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
Manyan Labarai

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Lawal
Labarai

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Lawal
Labarai

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Next Post
Ministan Wajen Sin: Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka Na Da Ma’anar Tarihi

Ministan Wajen Sin: Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka Na Da Ma'anar Tarihi

LABARAI MASU NASABA

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
Lawal

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Lawal

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.