ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ministan Wajen Sin: Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka Na Da Ma’anar Tarihi

by CGTN Hausa and Sulaiman
4 months ago
The U.S. and Chinese flag at the Great Hall of the People prior to the state dinner of President Donald Trump and Chinese President Xi Jinping on Thursday May 14, 2026, in Beijing. (AP Photo/Mark Schiefelbein)

Bisa gayyatar da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi masa, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gudanar da ziyara a kasar Sin tsakanin ranar Laraba da Juma’ar makon da muke ciki.

Daga baya a jiya Juma’a, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi wa manema labaru karin haske dangane da ganawar da shugabannin kasashen biyu suka yi a wannan karo.

A cewar jami’in na Sin, shugabannin kasashen Sin da Amurka sun yi musayar ra’ayi kan batun raya huldar dake tsakanin kasashensu, da al’amuran da ke faruwa a kasashe da shiyyoyi daban daban, wadanda ke jan hankalin al’ummun duniya, inda tattaunawar da suka yi ta nuna cewa, dukkan kasashen biyu za su iya cimma burinsu na raya kasa, ta hanyar baiwa junansu goyon baya, tare da haifar da alfanu ga al’ummun kasashe daban daban.

ADVERTISEMENT

Ban da haka, Wang Yi ya yi tsokaci kan matsaya daya da shugabannin kasashen Sin da Amurka suka cimma, game da kafa “dangantaka mai dorewa, da amfani bisa manyan tsare-tsare” tsakanin kasashensu.

Ya ce, wannan nau’in dangantaka ya shafi dora muhimmanci kan hadin gwiwar bangarorin 2, da yin takara a tsakaninsu bisa wani tsari mai dacewa, da kokarin cika alkawari, da neman tabbatar da zaman lafiya.Duk a wajen ganawar ta wannan karo, Wang Yi ya ce shugabannin kasashen biyu sun yarda da ci gaba da kokarin yin musayar ra’ayi tsakaninsu.

LABARAI MASU NASABA

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Kana bisa gayyatar da shugaba Trump ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyara kasar Amurka a lokacin kaka na bana. Ban da haka, kasashen 2 za su kara kokarin mu’ammala da juna, don neman daidaita huldar dake tsakaninsu ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, da karfafa cudanya a fannonin da suka shafi ilimi, da aikin yada labarai, da masana’antu, da kasuwanci, da dai makamantansu.Haka zalika, babban jami’in na kasar Sin ya ambaci wani batu mai muhimmanci da shugabannin biyu suka tattauna a kai, wato batun yankin Taiwan.

A cewar Wang Yi, matsayin kasar Sin dangane da lamarin a zahiri yake, wato na farko, batun yankin Taiwan batu ne na cikin gida na kasar Sin. Kana na biyu, batun Taiwan yana da matukar muhimmanci ga huldar dake tsakanin Sin da Amurka.

Sa’an nan, na uku, niyyar tabbatar da kwanciyar hankali a mashigin teku na Taiwan ta dace da burin kasashen Sin da Amurka na kare moriyar kansu.

Duk a wajen ganawar a cewar Wang Yi, shugabannin Sin da Amurka sun yi musayar ra’ayoyi dangane da batutuwan yankin Gabas ta Tsakiya da Ukraine, inda shugaba Xi Jinping ya jaddada bukatar komawa teburin shawarwari maimakon ci gaba da amfani da karfin tuwo, ta yadda za a samu damar gaggauta kawo karshen yake-yake. (Bello Wang)

Amurka
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Amurka
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta
  • Sulaiman
    Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen
  • Sulaiman
    Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
  • Sulaiman
    Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

MASU ALAKA

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen
Daga Birnin Sin

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
Daga Birnin Sin

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
Next Post
‘Ɗan Shekara 30’ Buba Ya Janye Daga Takarar Majalisar Wakilai

'Ɗan Shekara 30' Buba Ya Janye Daga Takarar Majalisar Wakilai

LABARAI MASU NASABA

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
Amurka

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Amurka

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.