Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya amince da yin ƙaramin sauyi a majalisar zartarwarsa, inda ya sauya wa wasu kwamishinoni ma’aikatunsu a wani yunƙuri na ƙarfafa tafiyar gwamnati a jihar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan, Humwashi Wonosikou, ya fitar a ranar Talata.
Gwamnan ya ce an yi sauye-sauyen ne domin ƙara sabon ƙwazo da kuzari ga gwamnati yayin da wa’adinta ke shiga zangon ƙarshe.
A cewar sanarwar, “An tsara sauye-sauyen ne domin samar da sabon ƙarfi ga zangon ƙarshe na gwamnati, kawo sabbin dabaru da kuma bai wa kwamishinoni ƙarin gogewa da fahimtar yadda gwamnati ke aiki a fannoni daban-daban.”















Discussion about this post