Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da ayyukan gina hanyoyi uku da za su haɗa ƙananan hukumomin Gusau, Bungudu, Kauran Namoda da Birnin Magaji.
Hanyoyin sun haɗa da Tashar Abu–Kekun Waje–Bingi, Kwatarkwashi–Mada, da Gusau–Jauri–Dogon Kade–Nasarawa Mai Layi–Nasarawa Godel.
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa an bai wa kamfanin Zhongcheng Construction Nigeria Limited aikin hanyar Kwatarkwashi zuwa Mada, wanda za a kammala cikin watanni 12. Haka kuma, kamfanin CCECC Nigeria Limited ne zai gina hanyar Gusau zuwa Nasarawa Godel mai tsawon kusan kilomita 53, wanda ake sa ran kammalawa cikin watanni 18. Yayin da aikin hanyar Tashar Abu zuwa Bingi ma zai ɗauki watanni 18.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da ayyukan, Gwamna Lawal ya ce inganta hanyoyi na daga cikin muhimman manufofin shirin gwamnatinsa na “Aikin Ceto”, domin bunƙasa tattalin arziki, inganta tsaro da sauƙaƙa rayuwar al’umma.
Ya bayyana cewa daga cikin kilomita 53 na hanyar Gusau zuwa Nasarawa Godel, kilomita biyar za su kasance a Gusau, 12 a Bungudu, tara a Kauran Namoda, yayin da Birnin Magaji za ta samu kilomita 27.
Gwamnan ya ce ayyukan za su haɗa al’ummomi da manyan biranen ƙananan hukumominsu da Gusau, tare da sauƙaƙa sufuri, rage kuɗin mota da taimaka wa manoma wajen kai amfanin gonakinsu kasuwa.













