ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, November 5, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abubuwa 6 Da Za Su Iya Haramta Maka Yin Zaɓe A Nijeriya

by Bello Hamza
9 hours ago
Zabe

Yayin da babban zaɓen Nijeriya na 2027 ke ƙara karatowa, masu kaɗa kuri’a na ta rubibi wajen ganin sun karɓi katunan zaɓensu domin samun damar zaɓar ɗan takarar da suke so.

Hukumar zaɓen Nijeriya dai ta sanar da fara raba katin zaɓe na dindindin a watan Oktoban da ya wuce.

A gefe ɗaya kuma, ƴan takara na ta yaƙin neman zaɓe domin tallata manufofinsu a wajen ‘ƴan Nijeriya.

ADVERTISEMENT

Sai dai, akwai wasu abubuwa da za su iya haramta wa mutum kaɗa kuri’a, kamar yadda dokar zaɓen Nijeriya ta bayyana.

Abubuwan da za su iya haramta wa mutum yin zaɓe sun kunshi:

LABARAI MASU NASABA

Matsin Tsadar Rayuwa A Nijeriya: Abubuwa 10 Da Suka Ƙara Tsada A Zamanin Tinubu

Shekara 20 Da Rasuwar Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido

‘Yan ƙasa da shekara 18

Dokar zaɓen Nijeriya da aka yi wa garambawul ta ginɗaya cewa duk ɗan ƙasar da bai kai shekara 18 ba, bai cika ka’idar yin zaɓe ba.

Don haka wannan rukuni na mutane na cikin waɗanda ba za su iya kaɗa kuri’a ba a Nijeriya.

Rashin yin rajista

Wane abu kuma da zai iya haramta wa mutum yin zaɓe shi ne rashin yin rajista a hukumar zaɓen Nijeriya.

Waɗanda ke tsare

Kawo yau, INEC ta bayyana cewa duk mutumin da ke tsare ba shi da hurumin yin zaɓe.

Hakan na nufin cewa duk mutum da ya aikata laifi sannan aka aika shi gidan yari ko kuma ke tsare a wurin ƴansanda, to kaɗa kuri’a ya haramta a kansa lokacin babban zaɓe.Ma’aikata na musamman

Ma’aikata na musamman ba su da damar zuwa wurin zaɓe don kaɗa kuri’a.

Duk da cewa doka ba ta haramta musu yin haka ba, amma yanayin aikinsu ba zai iya ba su damar zuwa rumfar zaɓe ba. Alal misali, ma’aikata kamar jami’an tsaro, ma’aikatan zaɓe, likitoci da kuma ‘ƴan jarida ba su da sukuni zuwa yin zaɓe.

‘Ƴan Nijeriya mazauna ƙasashen waje

Dokar zaɓen Nijeriya ba ta ware wa ‘ƴan ƙasar mazauna waje wani gurbi na kaɗa kuri’a ba lokacin yin zaɓe. Ana aika masu zaɓe zuwa wuri ɗaya ne kacal wato rumfar zaɓe don gudanar da zaɓe. Babu wanda yake da ikon yin zaɓe a wani wuri na daban, wanda ba hukumar zaɓe ce ta tanade shi ba.

Wanda ba a tantance ba

Ko da kana da katin rajistar zaɓe a Nijeriya, matuƙar ba a tantance ka a ranar zaɓe ba, ba za ka iya kaɗa ƙuri’a ba. Dokar zaɓe ta tanadi cewa wajibi ne mutum ya bi matakan da aka tsara wajen ganin an tantance shi kafin ya samu damar kaɗa ƙuri’a.

Zabe
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Matsin Tsadar Rayuwa A Nijeriya: Abubuwa 10 Da Suka Ƙara Tsada A Zamanin Tinubu
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Badakalar Rajistar Masu Zaɓe: Ezekwesili Ta Bukaci A Gudanar Da Bincike Mai Zaman Kansa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Hanyar Abuja-Kaduna: Ci Gaban Aikin Gyara Ya Farfaɗo Da Fatan Matafiya
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Tsadar Rayuwa: Yadda Iyalan Nijeriya Ke Komawa Abinci Mai Rahusa Domin Samun Sauƙin Rayuwa

MASU ALAKA

Tsadar Rayuwa: Yadda Iyalan Nijeriya Ke Komawa Abinci Mai Rahusa Domin Samun Sauƙin Rayuwa
Rahotonni

Matsin Tsadar Rayuwa A Nijeriya: Abubuwa 10 Da Suka Ƙara Tsada A Zamanin Tinubu

November 4, 2026
Shekara 20 Da Rasuwar Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido
Rahotonni

Shekara 20 Da Rasuwar Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido

November 1, 2026
Yarjejeniyar Zaman Lafiya
Rahotonni

2027: Yadda ‘Yan Siyasa Ke Amfani Da Matasa A Bangar Siyasa

November 1, 2026
Next Post
Nijeriya Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Kofin Duniya Na Mata U-17

Nijeriya Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Kofin Duniya Na Mata U-17

LABARAI MASU NASABA

ADC Ta Ɓoye Wajen Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Atiku A Sakkwato Saboda Matsalar Tsaro

APC Na Son Jefa Nijeriya Cikin Rikici – ADC

November 5, 2026
Tinubu Zai Tafi Saudiyya Domin Yi Wa Nijeriya Addu’a

Wane Tasiri Ƙarin Ciyo Bashin Dala Biliyan 7.7 Zai Yi A Kasafin Kuɗin Nijeriya Na Gaba?

November 5, 2026
Yadda Masu Amfani Da Moniepoint Za Su Karɓi Tallafin Naira 50,000 Na Gwamnatin Tarayya

Yadda Masu Amfani Da Moniepoint Za Su Karɓi Tallafin Naira 50,000 Na Gwamnatin Tarayya

November 5, 2026
Rikicin Siyasa: Shin ’Yan Takarar Jam’iyyun Adawa Suna Samun Tsaron Da Ya Dace A Yaƙin Neman Zaɓen 2027?

Rikicin Siyasa: Shin ’Yan Takarar Jam’iyyun Adawa Suna Samun Tsaron Da Ya Dace A Yaƙin Neman Zaɓen 2027?

November 5, 2026
Yadda Masu Amfani Da OPay Za Su Karɓi Tallafin Naira 50,000 Kyauta Daga Gwamnati

Yadda Masu Amfani Da OPay Za Su Karɓi Tallafin Naira 50,000 Kyauta Daga Gwamnati

November 5, 2026
Shirin Atiku Na Dawo Da Tallafin Mai Zai Dawo Da Nijeriya Baya Da Shekaru 20 — TSG

Atiku Ya Zargi APC Da Amfani Da Kotu Domin Raunana ADC

November 5, 2026
Hanyoyi 6 Da Masu Amfani Da ALAT By Wema Bank Za Su Bi Don Karɓar Tallafin Naira 50,000

Hanyoyi 6 Da Masu Amfani Da MoMo PSB Za Su Bi Don Karɓar Tallafin Naira 50,000

November 5, 2026
Hanyoyi 6 Da Masu Amfani Da ALAT By Wema Bank Za Su Bi Don Karɓar Tallafin Naira 50,000

Hanyoyi 6 Da Masu Amfani Da ALAT By Wema Bank Za Su Bi Don Karɓar Tallafin Naira 50,000

November 5, 2026
Hanyoyi 6 Da Masu Amfani Da Naira Gram Za Su Bi Don Karɓar Tallafin Naira 50,000

Hanyoyi 6 Da Masu Amfani Da Naira Gram Za Su Bi Don Karɓar Tallafin Naira 50,000

November 5, 2026
INEC Za Ta Cire Rajistar Masu Zaɓe Miliyan 1.5 Da Aka Gano Suna Da Kurakurai

INEC Za Ta Cire Rajistar Masu Zaɓe Miliyan 1.5 Da Aka Gano Suna Da Kurakurai

November 5, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.