Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da sabon shirin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na karɓar bashin waje na dala biliyan 7.7, kimanin kusan naira tiriliyan 10.79, yana mai gargaɗin cewa bashin zai ƙara wa ’yan Nijeriya da gwamnatocin da za su biyo baya nauyin da ke kansu.
Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Kwamitin Kamfen ɗinsa na Shugabancin Ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Laraba, inda ya bayyana yawan buƙatun karɓar bashi da Gwamnatin Tarayya ke gabatarwa a matsayin abin tayar da hankali.
Sabon bashin da ake nema, wanda ya kai kimanin Naira tiriliyan 10.79, ana sa ran za a yi amfani da shi wajen taimakawa wajen cike gibin kasafin kuɗin shekarar 2026.
Martanin ɗan siyasar adawar ya zo ne kwanaki kaɗan bayan gabatar da wani sabon shirin karɓar bashin waje na dala biliyan 20.52 da Yuro biliyan 1.045 ga Majalisar Dokokin Tarayya domin neman amincewarta.
Da yake tambayar tsarin da gwamnati ke bi wajen karɓar basussuka, Atiku ya ce bai kamata a sa ran ’yan Nijeriya za su ɗauki jerin buƙatun karɓar bashi da gwamnati ke gabatarwa a matsayin ayyukan majalisa na yau da kullum ba.













