Daga ranar 2 zuwa 5 ga Nuwamba, taron “Tattaunawar Masu Mukaman Magajin Gari na Duniya na 2026 a Ningbo”, mai taken “Bude kofar damarmarkin haduwa da juna da yin aiki cikin hadin gwiwa” ya gudana a birnin Ningbo na lardin Zhejiang, da ke kasar Sin.
Sama da mahalarta 260 ne suka halarci taron, ciki har da masu mukaman magajin gari da wakilan magajin gari daga birane 20 a fadin kasashe 15, da kuma wakilai daga kungiyoyi da kamfanoni na duniya, inda suka hallara don tattauna batutuwa kamar hadin gwiwar masana’antu, da bude kofar cinikayya, da musayar al’adu.
Tun bayan kaddamar da shi a shekarar 2024, an gudanar da taron “Tattaunawar Masu Mukaman Magajin Gari na Duniya” a birane daban-daban na kasar Sin, inda ya zama muhimmin dandali ga biranen kasar Sin da na kasashen waje, wajen musayar kwarewarsu ta shugabanci da kuma zurfafa hadin gwiwa a aikace. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)













