Rahotanni sun nuna cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya nemi a sauya kwamishinan ’yansandan jihar, CP Ibrahim Bakori, tare da maye gurbin manyan jami’an ’yansanda (DPO) su 18 da ke jagorantar sassa daban-daban na rundunar, gabanin zaɓen 16 ga Janairu, 2027.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa gwamnan ya gabatar da sunan sabon kwamishinan ’yansanda, CP Mohammed Yusuf Adamu, wanda aka ƙara masa girma kwanan nan, domin maye gurbin Bakori.
Majiyoyi sun ce matakin ya biyo bayan rashin jituwa tsakanin gwamnan da kwamishinan kan sauye-sauyen wuraren aiki da aka yi wa wasu manyan jami’an ’yansanda a jihar.
A cewar majiyoyin, Bakori ya sauya wasu jami’an DPO tare da maye gurbinsu da manyan jami’ai bisa la’akari da matsayi da ƙwarewar aiki. Sai dai rahoton ya ce matakin bai yi wa gwamnan daɗi ba.
Haka kuma, an ce Sufeto-Janar na ’Yansanda ya tura DPO 18 din da aka cire daga Kano zuwa jihohin Yobe, Gombe, Kebbi, Sokoto, Zamfara da Katsina.
Rahoton ya ƙara da cewa, hedikwatar rundunar ’yansandan kuma sai ta bayar da umarnin mayar da wasu jami’an da aka sauya zuwa wuraren aikinsu na baya, irin yadda gwamnan yake so.
Wuraren da sauye-sauyen ya shafa, sun hada da Fagge, Gwale, Ungogo, Kumbotso, Sharada, Bompai da Bichi.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yansanda ta ƙasa, Anietie Iniedu, ba ta amsa kiran waya da saƙon da aka aika mata ba.
Shima mai magana da yawun gwamnan Kano, Mustapha Mohammed, da aka nemi jin ta bakinshi, ya ce bai da masaniya kan lamarin.













