Firaministan kasar Sin, Li Qiang ya gana da darakta janar na hukumar kare hakkin mallakar fasaha ta duniya (WIPO), Daren Tang, a birnin Beijing, yau Laraba 4 ga watan Nuwamba.
Li Qiang ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta ci gaba da hadin gwiwa da WIPO wajen gina kwazon aiki, da nufin cimma burikan kasashe maso tasowa, da sanar da juna kwarewa mai amfanarwa, da bayar da karin gudummawar abubuwa masu kyau ga jama’a, da kuma tabbatar da cewa nasarorin da aka samu wajen bunkasa fasaha sun amfanar da dukkan bangarori.
A nasa bangare, Daren Tang, ya bayyana cewa, kasar Sin tana cikin manyan kasashe goma da ke cikin jerin masu fasahar kirkire-kirkire na duniya, kuma tana da kaso mafi yawa a cikin jerin rukunonin sabbin kirkire-kirkire guda 100 da ke sahun gaba a duniya, kana tattalin arzikinta na sabbin kirkire-kirkire, ciki har da fina-finai da wasanni, yana ci gaba da bunkasa cikin sauri. Kwarewar da kasar Sin ta samu a fannin bunkasa abubuwa na fasaha ta samar da darussa masu amfanarwa ga sauran kasashe. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)













