ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, November 6, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Dauda Ya Amince Da Ɗaukar Ƙarin Ƙwararrun Ma’aikata 75 A Hukumar Haraji Ta Zamfara

by Sulaiman
1 day ago
Haraji

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da ɗaukar ƙarin ƙwararrun ma’aikata a sassa daban-daban na Hukumar Tara Haraji ta Cikin Gida ta Jihar Zamfara (ZIRS), a wani mataki na ƙarfafa hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga ga gwamnatin jihar.

Sanarwar da Mai Magana da Yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar 4 ga Nuwamba, 2026, ta ce hukumar ta fara aikin ɗaukar ma’aikatan ne bisa ƙa’idojin yawan ma’aikatan da ake buƙata da kuma dokokin aikin gwamnati.

Sanarwar ta ce, ɗaukar ma’aikatan na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Dauda Lawal na inganta ayyukan hukumar da kuma ƙara ƙarfin tattara kuɗaɗen shiga na cikin gida domin bunƙasa jihar.

ADVERTISEMENT

Ma’aikatan da za a ɗauka za su yi aiki ne a fannoni daban-daban da suka haɗa da gudanar da harkokin haraji, ayyukan shari’a, wayar da kan jama’a, yaɗa labarai, ɗaukar hoto da kuma fasahar sadarwa da na’ura mai ƙwaƙwalwa.

An gudanar da rubutaccen jarrabawar tantance masu neman aikin ne a ranar 11 ga Yuli, 2026, inda mutane 484 suka halarta.

LABARAI MASU NASABA

Obi Ya Soki Hukuncin Kotu Kan Soke Takarar Atiku A ADC

Gwamnan Zamfara Ya Raba Motoci 300 Da Babura 2,000 Ga Ƙungiyoyi Da Ɗaiɗaikun Mutane A Gusau

Kwamitin da aka kafa domin gudanar da aikin ɗaukar ma’aikatan ne ya tantance amsoshin jarrabawar, ba tare da dogaro da wani ɓangare na waje ba.

A yayin tantance masu neman aikin, an duba cancantar karatunsu da ƙwarewar aikinsu, iya sadarwa, ƙwarewar fasaha, yadda suke gabatar da kansu, halayensu da kuma iliminsu a fannonin daban-daban.

Bayan kammala dukkan matakan tantancewa, waɗanda suka haɗa da tattara sakamakon jarabawa da tabbatar da sahihancinsa, an zaɓi mutane 75 da suka yi nasara domin ba su guraben aikin.

Hukumar Tara Haraji ta Cikin Gida ta Jihar Zamfara ta jaddada cewa an gudanar da zaɓen ne bisa cancanta da ƙwarewar ’yan takara, bin sharuɗɗan da aka sanar tun farko, tantance sahihancin takardun shaidar karatu da ƙwarewa, tare da tabbatar da adalci da gaskiya a dukkan matakan aikin.

Haraji
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    An Gudanar Da Taron Tattaunawa Mai Jigon “Jagorancin Kasar Sin Da Ci Gaban Duniya” A Kuwait
  • Sulaiman
    Gwamnan Zamfara Ya Raba Motoci 300 Da Babura 2,000 Ga Ƙungiyoyi Da Ɗaiɗaikun Mutane A Gusau
  • Sulaiman
    Wang Huning Ya Yi Kira Ga Mabiya Addinin Dao Su Ba Da Gudunmuwa Ga Gina Al’umma Mai Makoma Ta Bai Daya Ga Dan Adam
  • Sulaiman
    Ra’ayin Sin Game Da Kimiyya Da Fasaha: Bude Kofa Ga Juna Da Kuma Amfanar Da Kowa

MASU ALAKA

Obi Ya Soki Hukuncin Kotu Kan Soke Takarar Atiku A ADC
Manyan Labarai

Obi Ya Soki Hukuncin Kotu Kan Soke Takarar Atiku A ADC

November 5, 2026
Gwamnan Zamfara Ya Raba Motoci 300 Da Babura 2,000 Ga Ƙungiyoyi Da Ɗaiɗaikun Mutane A Gusau
Labarai

Gwamnan Zamfara Ya Raba Motoci 300 Da Babura 2,000 Ga Ƙungiyoyi Da Ɗaiɗaikun Mutane A Gusau

November 5, 2026
Ra’ayin Sin Game Da Kimiyya Da Fasaha: Bude Kofa Ga Juna Da Kuma Amfanar Da Kowa
Daga Birnin Sin

Ra’ayin Sin Game Da Kimiyya Da Fasaha: Bude Kofa Ga Juna Da Kuma Amfanar Da Kowa

November 5, 2026
Next Post
Taron Tattaunawar Magajin Gari Na Duniya Na 2026 A Ningbo Ya Kasance Na Bude Kofa Da Haduwa Da Juna Da Hadin Gwiwar Birane

Kasar Sin Na Kara Azamar Aiwatar Da Matakan Kare Yanayi

Kasar Sin Na Kara Azamar Aiwatar Da Matakan Kare Yanayi

November 5, 2026
An Bude Bikin Baje Kolin CIIE Karo Na 9 A Shanghai

An Bude Bikin Baje Kolin CIIE Karo Na 9 A Shanghai

November 5, 2026
ADC Ta Ɓoye Wajen Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Atiku A Sakkwato Saboda Matsalar Tsaro

APC Na Son Jefa Nijeriya Cikin Rikici – ADC

November 5, 2026
Hadin Gwiwar Makamashi Mai Sabuntawa Tsakanin Sin Da Afirka Na Hanzarta Samun Ingantaccen Ci Gaba

Hadin Gwiwar Makamashi Mai Sabuntawa Tsakanin Sin Da Afirka Na Hanzarta Samun Ingantaccen Ci Gaba

November 5, 2026
Tinubu Zai Tafi Saudiyya Domin Yi Wa Nijeriya Addu’a

Wane Tasiri Ƙarin Ciyo Bashin Dala Biliyan 7.7 Zai Yi A Kasafin Kuɗin Nijeriya Na Gaba?

November 5, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.