Shugaban Kamfanin Dangote Industries Limited, Alhaji Aliko Dangote, ya ce ci gaba da safarar man fetur zuwa ƙasashen makwabta ba bisa ƙa’ida ba na daga cikin dalilan da ke sa farashin man fetur ke cigaba da kasancewa mai tsada a Nijeriya.
Dangote ya bayyana cewa farashin man fetur a ƙasashen da ke makwabtaka da Nijeriya ya fi na Nijeriya da kashi 30 zuwa 50 cikin 100, lamarin da ya ce ke bai wa ’yan kasuwa babbar damar samun riba ta hanyar fitar da man fetur daga Nijeriya.
Ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Arise TV a ranar Talata, yayin da yake magana kan farashin man fetur da kuma samuwar sa a Nijeriya a daidai lokacin da ake fama da rikicin Gabas ta Tsakiya.
Dangote ya ce duk da cewa Nijeriya na samar da man fetur a cikin gida, ba za a iya kallon farashin man ba tare da la’akari da farashin da ake sayar da shi a ƙasashen makwabta ba.
Ya ƙara da cewa bambancin farashin na ƙara ƙarfafa safarar man fetur zuwa ƙasashen waje, wanda ke shafar farashi da wadatar man a cikin Nijeriya.
ADVERTISEMENT













