ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Zamfara Ta Jaddada Aniyarta Na Ƙin Sulhu Da ‘Yan Ta’adda

by Sulaiman
3 months ago
Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake jaddada matsayar gwamnatin sa na ƙin shiga tattaunawa ko ƙulla yarjejeniyar sulhu da ’yan bindiga, yana mai cewa gwamnatin jihar ba za ta amince da zaman sulhu da ƙungiyoyin masu aikata laifuka ba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Sashen Hausa na BBC, wadda aka saurara a Kaduna, inda ya ce gwamnatinsa na ci gaba da goyon bayan dabarar yaƙi da rashin tsaro ta hanyar amfani da jami’an tsaro maimakon tattaunawa da masu aikata laifuka.

Dauda Lawal ya ce ba abin yarda ba ne ga kowane mutum ko ƙungiya ta shiga tsakani wajen ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da ’yan bindiga, yana mai jaddada cewa duk wanda ke yin hakan yana yi ne a madadinsa ba tare da wakiltar gwamnatin jihar ba.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, tun daga farkon mulkinsa gwamnati ta tsaya tsayin daka kan cewa ba za ta yi sulhu da ƙungiyoyin da ke da alhakin kashe-kashe, garkuwa da mutane da kai hare-hare kan al’ummomi a faɗin jihar ba.“Ra’ayin neman sulhu da ’yan bindiga ba ra’ayina ba ne, kuma ba zai taɓa zama haka ba,” in ji gwamnan, yana mai jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta yi sassauci da masu aikata laifuka ba.

Gwamnan ya bayyana cewa wasu rahotannin da ke yawo kan cewa an samu yarjejeniyar sulhu a wasu sassan jihar ba su samu amincewar gwamnatin Zamfara ba.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Ya ce gwamnatin jihar ba ta da hannu a irin waɗannan shirye-shirye, kuma ba ta sauya matsayarta kan yadda za a magance matsalar tsaro ba.

Lawal ya nuna cikakken kwarin gwiwa kan cewa jami’an tsaro za su iya kawo ƙarshen ayyukan ’yan bindiga, yana mai cewa babu wata ƙungiyar masu laifi da ta fi ƙarfin gwamnatin Najeriya.“Gwamnati ta fi ƙarfin kowace ƙungiyar ’yan bindiga,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa ci gaba da gudanar da hare-haren tsaro tare da haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.

Gwamnan ya tunatar da cewa an yi ƙoƙarin yin sulhu da ’yan bindiga a baya, amma hakan bai samar da mafita ba.A maimakon haka, ya ce irin waɗannan yarjejeniyoyi sun ƙara wa masu aikata laifukan ƙarfin guiwa tare da ba su damar ci gaba da ayyukansu.

A cewarsa, dabarar tsaron da ake aiwatarwa yanzu a Zamfara ta fara nuna sakamako mai kyau, inda wasu yankunan da a baya suka yi ƙaurin suna wajen hare-haren ’yan bindiga suka fara samun kwanciyar hankali sakamakon ƙara zafafa ayyukan soji.

Dauda Lawal ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da nuna haƙuri tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai a yaƙin da ake yi da rashin tsaro.

Ya tabbatar musu da cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen lalata hanyoyin sadarwa da sansanonin masu aikata laifuka.Gwamnan ya sake nanata cewa hanya mafi dacewa ta samar da zaman lafiya mai ɗorewa a Zamfara ita ce ɗaukar mataki mai tsauri kan ’yan bindiga, ba ta hanyar shiga tattaunawar sulhu da su ba.

Zamfara
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace
  • Sulaiman
    Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum
  • Sulaiman
    Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO
Labarai

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Next Post
An Bude Bikin Baje Kolin Hada-Hadar Samar Da Kayayyaki Ta Kasa Da Kasa Karo Na Hudu

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.