ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Zamfara Ta Tantance Makarantu Masu Zaman Kansu 242, Ta Kwato Bashin Harajin Naira Miliyan 23

by Sulaiman
5 days ago
Zamfara

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce ta amince da makarantun masu zaman kansu 123 bayan sun cika mafi ƙarancin ƙa’idojin koyarwa da ilmantar da yara da aka gindaya a jihar.

Gwamnatin jihar ta ce, ta gano makarantu masu zaman kansu 508 da ke aiki a faɗin jihar, inda aka tantance 242 daga cikinsu a fannoni daban-daban domin tabbatar da cewa suna bin ƙa’idojin da jihar ta shimfiɗa na koyarwa da ilmantarwa.

Shugabar Kwamitin Tilasta Bin Ƙa’idojin Mafi Ƙarancin Matsayi da Kula da Ayyukan Makarantu Masu Zaman Kansu, Kulu Na’ala, ce ta bayyana hakan a ranar Talata a Gusau, yayin gabatar da rahoton kwamitin.

ADVERTISEMENT

Ta ce daga cikin nauyin da aka ɗora wa kwamitin akwai tabbatar da cewa makarantun masu zaman kansu sun cika sharuddan da suka dace domin gudanar da ayyukansu cikin aminci, bin doka da kuma samar da ingantaccen ilimi, bisa tsarin manufofin gwamnatin jihar kan harkar ilimi.

Na’ala ta ce daga cikin makarantu 508 da aka gano, an tantance 242, inda aka samu makarantu 123 da suka cika ƙa’idojin da ake buƙata, yayin da aka sanya makarantu 119 cikin rukunin waɗanda suka samu matsakaicin sakamako ko kuma suka kasa cika wasu daga cikin ƙa’idojin da aka gindaya.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Ta ce kwamitin ya samu nasarori masu muhimmanci yayin aikin tantancewar, ciki har da kwato bashin haraji da ya kai naira miliyan 23, wanda aka miƙa wa Hukumar Tattara Harajin Cikin Gida ta Jihar Zamfara.

Shugabar kwamitin ta ce an kuma horas da masu makarantu kan yadda za su samar da takardun neman biyan haraji da kuma amfani da hanyoyin biyan kuɗi ta na’ura, domin rage ɓarnar kuɗaɗen shiga da kuma tabbatar da cewa kuɗin haraji sun shiga asusun gwamnati yadda ya kamata.

Ta ƙara da cewa an kammala samar da ingantaccen tsarin tantance makarantu ta hanyar na’ura, wanda ke ba da maki ga makarantu tare da nuna matakin da kowace makaranta ta kai da kuma shawarwarin da ya kamata a bi domin inganta ayyukanta.

A cewarta, kwamitin ya kuma samar da cikakken kundin bayanai na makarantun masu zaman kansu, wanda za a riƙa amfani da shi a ayyukan tantancewa na gaba.

Ta ce hakan zai taimaka wajen ƙara wayar da kan masu makarantu game da mafi ƙarancin ƙa’idojin da ake buƙata, kare haƙƙin yara, tabbatar da ingancin ilimi da kuma inganta adana bayanan makarantu.

Sai dai Na’ala ta bayyana rashin ingantacciyar doka da ke kula da ayyukan makarantun masu zaman kansu a jihar a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ke kawo cikas ga ingantaccen sa ido da tsara harkokinsu.

Ta ce kuma akwai ruɗani kan irin ayyukan da takardar amincewar gudanar da makaranta ta ba wa wasu makarantu damar yi, lamarin da ke sa aiwatar da dokokin kula da su ya zama da wahala.

“Har yanzu akwai makarantu da ke aiki ba tare da takardar amincewar gwamnati ba, kuma wannan batu na buƙatar a gaggauta magance shi,” in ji ta.

Na’ala ta sake jaddada aniyar kwamitin na tabbatar da cewa dukkan makarantun masu zaman kansu sun bi ƙa’idojin da gwamnati ta gindaya, tana mai gargadin cewa makarantar da ta ƙi bin ƙa’idojin na iya fuskantar soke rajistarta da kuma hana ta ci gaba da aiki.

Ta kuma ce gwamnati na nan daram wajen tabbatar da an biya dukkan wajibcin haraji domin ƙara wa kuɗaɗen da ake warewa harkar ilimi ƙarfi.

Sai dai ta yi kira da a samar da ingantattun dokoki da za su ba hukumomi damar aiwatar da waɗannan matakai yadda ya kamata, tare da sauƙaƙa tsarin amincewa da makarantun, da kuma ƙara sa ido kan cibiyoyin koyarwa da ke aiki a wajen tsarin ilimi na hukuma.

Zamfara
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Mutane 43 Sun Mutu A Wajen Rikicin Satar Mai A Ribas

Mutane 43 Sun Mutu A Wajen Rikicin Satar Mai A Ribas

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.