Hukumar Jin dadin Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta samu nasarar ƙarin kujerun aikin Hajji guda 10,000 daga mahukuntan Ƙasar Saudiyya, lamarin da ya sa jimillar adadin kujerun da aka ware wa Nijeriya domin aikin Hajjin bana ya kai 60,000.
Wannan ƙari ya biyo bayan tattaunawa mai zurfi da kuma ƙoƙarin da hukumar ta yi tare da Ma’aikatar Aikin Hajji da Umra ta Saudiyya, domin bai wa ƙarin maniyyata a Nijeriya damar sauke farali bayan kason farko na kujeru 50,000 da aka ware wa ƙasar ya cika.
NAHCON ta bayyana cewa za a raba sabbin kujerun da aka samu cikin adalci tsakanin hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi da kuma kamfanoni masu zaman kansu da ke shirya aikin Hajji (tour operators), domin magance ƙarancin kujeru ga maniyyatan da ke jiran tsammani a faɗin ƙasar.

Haka kuma, hukumar ta buƙaci hukumomin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta kammala tantancewa tare da shigar da bayanan maniyyatan da suka cancanta cikin tsarin da aka tanada, domin bin ƙa’idoji da jadawalin da mahukuntan Saudiyya suka gindaya a kan lokaci.
A ƙarshe, NAHCON ta sake jaddada aniyarta ta tabbatar da ganin mahajjatan Nijeriya sun sami kyakkyawar kulawa, da masauki mai inganci, da sauran hidimomin da suka dace a ƙasa mai tsarki, domin gudanar da aikin Hajjin cikin nasara da sauƙi.













