ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Halin Rigakafin Annoba A Amurka Yana Da Ban Tsoro, Ta Yaya Za Ta Nuna Yatsa Ga Saura?

by CMG Hausa
4 years ago
Amurka

Bisa kididdigar da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Amurka ta fitar, kasar Amurka ta fuskanci bala’in annobar COVID-19 har sau biyar a cikin shekaru uku da suka gabata. Kuma a duk lokacin da adadin masu kamuwa da cutar ya kai matsayin koli, ana samun rahotanni masu yawa, game da yadda ake samun kusan rugujewar tsarin aikin likitancin kasar.

Sakamakon sakaci da aiki da gwamnatin Amurka ke yi, kusan dukkanin nau’ikan cutar COVID-19 sun taba yaduwa a kasar, wanda hakan ya haddasa harbuwar mutane sama da miliyan 100 a kasar, kana sama da mutane miliyan 1.08 sun mutu, baya ga yara 250,000 da suka zama marayu saboda kisan da annobar ta yi, inda matsanancin halin da kasar ke ciki ya sanya ta kan gaba a fannin fama da cutar a duniya.

  • Sin Ta Inganta Inshorar Likitanci Don Saukaka Kudaden Da Masu Fama Da Cutar COVID-19 Ke Kashewa

Wasu manazarta sun yi nuni da cewa, ainihin abin da ya haifar da yanayin da ake ciki shi ne, yadda gwamnatin Amurka ba ta taba sadaukar da karfinta ga aikin magance hakikanin matsalolin da take da fuskanta ba, maimakon hakan tana ta siyasantar da batun annobar.

ADVERTISEMENT

Sabanin haka, kasar Sin ta aiwatar da matakai daban daban a cikin shekarun ukun da suka gabata, inda ta aiwatar da tsauraran manufofin rigakafi, da shawo kan cutar a lokacin da ake shan fama da ita, ta jure jarrabawar yaduwar annobar har sau biyar, kana da rage yawan wadanda suka nuna alamu masu tsanani ko kuma mace-mace a sakamakon cutar. Har ila yau, ta samu lokaci mai muhimmanci na nazarin magunguna, da alluran rigakafin cutar.

Kamar sauran kasashe, kasar Sin ma na bukatar wani lokaci na daidaitawa, wajen kyautata manufofin rigakafin cutar. Musamman yadda kasar Sin ke da yawan al’umma da yawan tsofaffi, don haka babu makawa, kasar na fuskantar wasu matsaloli, ciki har da karuwar adadin masu kamuwa da cutar, da masu bukatar magani. Amma duk da haka, gwamnatin kasar Sin ba ta taba yin kasa a gwiwa ba, wajen sanya himmar warware matsalolin ta. Bugu da kari, a cewar mai tsara shirye-shiryen documentary dan kasar Burtaniya Malcolm Clarke, wanda ya taba zama a kasar Sin tsawon shekaru uku da suka gabata, “Na kasance mai cin gajiyar kokarin da Sin ke yi na kare rayuka da lafiyar jama’a.”

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Daga yau 8 ga watan Janairu na shekarar bana, kasar Sin ta sassauta matakanta na yaki da cutar COVID-19 daga rukunin A zuwa rukunin B, don haka ta daina daukar matakan binciken cutar ba kan matafiya da kayayyaki dake shigowa daga ketare. Wannan shi ne kokarin da kasar Sin ta yi na baya-bayan nan, don inganta manufofin kandagarkin annobar bisa lokaci da yanayin da ake ciki, wanda hakan sauke nauyin al’ummar kasar ne, kuma yana taimakawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

Amurka
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Abba Gida-Gida Ya Maka Shugaban APC Na Kano A Kotu Kan Kalaman Tunzura Mutane

Ba Zan Kai 'Ya'yana Karatu Waje Ba Idan Na Zama Gwamnan Kano - Abba Gida-Gida

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.