Majalisar Dokokin ta Ƙasa ta aika wa Majalisun Dokokin Jihohi 36 kudirin gyaran Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na shekarar 1999, wanda ya shafi kafa Rundunar Ƴansandan Jihohi. Sai dai ba dukkan kudurorin gyaran kundin tsarin mulki 37 da ake nazari ba ne aka aika wa jihohin. Wannan shi ne kudirin da ya zuwa yanzu majalisun biyu na tarayya suka amince da shi.
1. Ƴansandan Jihohi Ne Kawai Aka Aika: Kudirin da aka aika wa majalisun jihohi shi ne wanda zai ba da damar kafa rundunonin ƴansanda na jihohi.
2. Ba A Aika Dukkan Kudurorin 37 Ba: Duk da cewa kudurorin gyaran kundin tsarin mulki 37 sun bi matakai daban-daban, ciki har da sauraron ra’ayoyin jama’a, kudirin ƴansandan jiha ne kaɗai ya kammala matakin da ya ba da damar aika shi ga jihohi.
3. Jihohi 24 Ne Dole Su Amince: Sashi na 9 na Kundin Tsarin Mulki ya tanadi cewa dole ne a samu amincewar aƙalla kashi biyu cikin uku na Majalisun Dokokin Jihohi 36, wato jihohi 24, kafin gyaran ya iya samun tabbatuwa.
4. Kowace Jiha Za Ta Bi Tsarinta: Majalisun dokokin jihohi za su duba kudirin bisa tsarin dokokin majalisunsu, sannan su sanar da Majalisar Dokokin Ƙasa matsayarsu bayan kammala nazari.
5. Kwanaki 30 Ba Wa’adi Ne Na Kundin Tsarin Mulki Ba: Majalisar Dokokin Ƙasa ta bukaci jihohi su sanar da matsayarsu cikin kwanaki 30 daga ranar da suka karɓi kudirin. Sai dai ta bayyana cewa wannan wa’adi ne na gudanarwa kawai, ba wa’adin da Kundin Tsarin Mulki ya tanada ba.
6. Za A Samu Tsarin Ƴansanda Biyu: Idan aka amince da gyaran, Nijeriya za ta samu Rundunar Ƴansandan Tarayya da kuma Rundunonin Ƴansandan Jihohi, maimakon tsarin da ake da shi na rundunar ƴansanda guda ɗaya da ke ƙarƙashin tsarin tarayya.
7. Ƴansandan Jiha Za Su Yi Aiki A Cikin Jihohinsu: Babban aikin rundunar ƴansandan kowace jiha zai kasance kula da tsaro da lafiyar jama’a a cikin jihar da aka kafa ta.
8. Ba Za Su Yi Aiki A Wata Jiha Kai Tsaye Ba: Rundunar ƴansandan jiha ba za ta samu ikon gudanar da ayyukan ƴansanda a wajen iyakar jihar ba, sai idan wata dokar Majalisar Dokokin Ƙasa ta ba ta wannan dama.
9. Ƴansandan Tarayya Za Su Ci Gaba Da Kula Da Manyan Laifuka: Rundunar Ƴansandan Tarayya za ta riƙe alhakin manyan harkokin tsaron ƙasa, ciki har da ta’addanci, da laifukan yanar gizo, da laifukan da suka shafi jihohi daban-daban, da safarar makamai da ƙungiyoyin manyan laifuka na ƙasa da ƙasa.
10. Wasu Kudurorin Gyara Suna Nan A Majalisar: Daga cikin sauran shawarwarin da ake nazari akwai cin gashin kan ƙananan hukumomi, da kujerun musamman ga mata a majalisa, da takarar kai tsaye ba tare da jam’iyya ba (indifenda), da sake fasalin tsarin zaɓe, da sauye-sauyen shari’a da kuma ƙarin iko ga ƙananan hukumomi.
11. Akwai Shawarwarin Ƙirƙirar Sabbin Jihohi Da Ƙananan Hukumomi: Wasu daga cikin kudurorin da ke jiran kammala matakan majalisa sun shafi ƙirƙirar sabbin jihohi da ƙananan hukumomi, da kuma wasu sauye-sauye kan tsarin gudanar da mulki.
12. Matakin Jihohi Shi Ne Na Gaba: Bayan Majalisun Dokokin Jihohi sun kammala nazarin kudirin tare da tura matsayarsu ga Majalisar Dokokin Ƙasa, za a ci gaba da sauran matakan da Kundin Tsarin Mulki ya tanada domin kammala aikin gyaran.














