ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Cafke Ɗalibai 6 A Kogi Bisa Zargin Kai Hari A Harabar Makaranta

by Rabi'u Ali Indabawa
5 months ago

Rundunar ƴansandan Jihar Kogi ta kama ɗalibai shida na Jami’ar Tarayya ta Lokoja bisa zargin aikata (bibiyar mutum ta Intanet da cin zarafi). Ɗaliban da aka kama sun haɗa da Inajo Henry, Nzekwe Ɓictor, Lucky Ɓictor, Lucky Gambo da Paul Daɓid, tare da wani mutum guda (yaro mai shekaru 17), dukkansu ɗalibai maza na Jami’ar Tarayya ta Lokoja.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, ASP Saliu Oyiza Afusat, ta fitar a ranar Talata, ta ce an kama su ne bayan wani ɗalibi namiji ya kai ƙorafi kan cin zarafi ta Intanet. Ta ce, “Rundunar ƴansandan Jihar Kogi na sanar da jama’a cewa a ranar 30 ga Maris, 2026, an kawo rahoton haɗa baki wajen aikata laifi, amfani da ƙarfi ba bisa ƙa’ida ba, ɓata suna, kai hari, da kuma cyberstalking a ofishin ‘B’ Diɓision, Lokoja, daga wani Oladosu Sunday, ɗalibi a Jami’ar Tarayya ta Lokoja.”

  • Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
  • Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Ta ƙara da cewa daga baya aka miƙa shari’ar zuwa sashen binciken manyan laifuka na jiha domin gudanar da cikakken bincike cikin sirri.

ADVERTISEMENT

Bisa ga bayaninta, bayan bincike mai zurfi, rundunar ta kama waɗanda ake zargi: Inajo Henry, Nzekwe Ɓictor, Lucky Ɓictor, Lucky Gambo da Paul Daɓid, tare da wani yaro mai shekaru 17, dukkansu ɗalibai maza.

Ta ce binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin, ba tare da wata hujja mai inganci ba, sun zargi Oladosu Sunday da zama ɗan luwadi, sannan suka shirya yadda za su jawo shi zuwa gidansu da ke kusa da yankin Liɓing Faith Church a Felele, Lokoja, a ranar 29 ga Maris, 2026, da misalin ƙarfe 9:00 na dare.

LABARAI MASU NASABA

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

An bayyana cewa sun ƙulle shi a cikin ɗaki, suka tuɓe masa kaya da ƙarfi, sannan suka yi masa mugun duka da bel da wayoyin caja, yayin da suke ɗaukar bidiyo.

Ta ce daga baya an yaɗa bidiyon a intanet, inda ya bazu a tsakanin ɗaliban jami’ar.

Ta ƙara da cewa waɗanda ake zargin sun amsa laifin yayin tambayoyi, inda suka ce sun shirya aikata hakan ne tun da farko bisa zargi marar tabbaci game da halayen wanda aka cutar.

Mai magana da yawun rundunar ta ce an kammala bincike, kuma an gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotun da ta dace.

Rundunar ta sake jaddada cewa ba za ta amince da ɗaukar doka a hannu, cin zarafi ta yanar gizo, ko duk wani nau’in laifi ba.

Ta gargaɗi jama’a, musamman matasa da ɗalibai, da su guji ɗaukar doka a hannu ko aikata ayyukan da ke take haƙƙin ɗan ‘Adam da mutuncin wasu, tare da shawartar masu ƙorafi da su bi hanyoyin doka wajen neman haƙƙinsu.

Ta tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kare haƙƙin kowa da kuma tabbatar da hukunta masu laifi.

Kwamishinan ƴansandan jihar, Naziru Bello Kankarofi, ya tabbatar wa al’ummar Jihar Kogi ƙudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyi, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da ba da haɗin kai wajen yaƙi da laifuka.

Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Tsaro

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

July 11, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’
Tsaro

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

July 9, 2026
Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara
Tsaro

Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara

June 25, 2026
Next Post
Yawan Kuɗaɗen Da Ke Wajen Bankuna Sun Ragu Zuwa Kashi 3.66 A Watan Fabrairu

Yawan Kuɗaɗen Da Ke Wajen Bankuna Sun Ragu Zuwa Kashi 3.66 A Watan Fabrairu

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.