ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Harin Maiduguri: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Saƙon Trump A Kan Tinubu

by Sadiq
6 months ago
Tinubu

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce saƙon da ya karaɗe kafafen sada zumunta, wanda ke iƙirarin cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya soki Shugaba Bola Tinubu kan hare-haren Maiduguri, ba gaskiya ba ne.

Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ya bayyana sakon a matsayin “ƙarya!!!” a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata.

  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Allah-wadai Da Hare-haren Ƙunar Baƙin Wake A Maiduguri
  • Manyan Ma’aunan Tattalin Arzikin Sin Sun Karu Daga Janairu Zuwa Fabrairu

Ya kuma wallafa hoton saƙon domin gargaɗin jama’a kan yaɗa labaran ƙarya.

ADVERTISEMENT

A cikin saƙon an bayyana cewa Trump ya zargi Tinubu da gazawa wajen magance matsalar tsaro a Arewa maso Gabas, tare da sukar tafiyarsa zuwa Birtaniya a lokacin da hare-haren a ƙasar.

Haka kuma saƙon ya ce Trump ya nemi Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, da ya umarci Tinubu ya dawo Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Sai dai bincike ya nuna cewa Trump bai fitar da wannan bayani a shafukansa ba.

Wannan jita-jitar ta yaɗu ne a lokacin da ake cikin damuwa bayan hare-haren Maiduguri.

Da yammacin ranar Litinin, wasu da ake zargi ‘yan ƙunar baƙin wake ne sun kai hare-hare a wurare daban-daban na birnin, ciki har da wuraren da jama’a ke taruwa.

‘Yansanda sun ce aƙalla mutane 23 sun mutu, yayin da sama da 100 suka jikkata.

Hare-haren sun biyo bayan wani harin da aka kai wani sansanin sojoji a yankin Ajilari.

Shugaba Tinubu ya bayyana hare-haren a matsayin “abin takaici matuƙa”, yana mai ɗora laifi kan ƙungiyoyin ta’addanci da ke fuskantar matsin lamba daga dakarun Nijeriya.

Ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu, ya kuma tausaya wa waɗanda suka jikkata, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da tsaro.

Haka kuma ya umarci shugabannin tsaro su koma Maiduguri domin jagorantar ayyukan tsaro, yana mai cewa Nijeriya ba za ta yarda ta’addanci ya yi tasiri ba.

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Dalilin Da Ya Sa Sin Ta Samu Ci Gaban Tattalin Arziki Mai Kyau A Watanni 2 Na Farkon Bana

Dalilin Da Ya Sa Sin Ta Samu Ci Gaban Tattalin Arziki Mai Kyau A Watanni 2 Na Farkon Bana

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.