Manoma biyar, maza huɗu da mace ɗaya, sun mutu bayan wani jirgin ruwa ya kife da su a Kogin Kudi, da ke Ƙaramar Hukumar Katcha ta Jihar Neja.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Shaba-Woshi-Kpaya, da ke Gundumar Edotsu, a yammacin ranar Asabar.
Wani mazaunin yankin, Muhammadu Dan-Asabe, ya shaida wa Daily Trust cewa waɗanda abin ya rutsa da su suna kan hanyarsu ta zuwa gonakinsu ne lokacin da kwale-kwalen ya kife.
Daraktan Yaɗa Labarai da Ayyuka na Musamman na Hukumar Kula da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Dr Ibrahim Audu Hussaini, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce mutanen suna tafiya ne daga ƙauyensu zuwa gonakinsu lokacin da ibtila’in ya faru.An bayyana sunayen waɗanda suka rasu da Yahaya Abubakar, Usman Abubakar, Lami Hussaini, Baba Ahmadu da Salihu Aliyu.
Hussaini ya ce an gano gawarwakin mutanen biyar tare da binne su a ranar Asabar.














