Aƙalla mutane 22, ciki har da Babban Limamin Masallacin Jumu’a na Izala dake Ungushi, Imam Aliyu, ne aka kashe a wani hari da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai wa al’ummar Ungushi, da ke Ƙaramar Hukumar Kebbe ta Jihar Sokoto.
Rahotanni sun ce an kashe mutanen ne yayin harin da maharan suka kai wa al’ummar garin a yammacin ranar Lahadi, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin fargaba tare da ƙara haifar da damuwa kan taɓarɓarewar tsaro a yankin.
Majiyoyi daga al’ummar garin sun ce maharan sun shiga Ungushi tare da buɗe wa mazauna garin wuta, inda suka kashe mutane da dama, ciki har da malamin addinin Musulunci.Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce sabon harin ya jefa al’ummar cikin tsananin baƙin ciki da ruɗani.
Wani mazaunin ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su gaggauta ƙara yawan jami’an tsaro a Ungushi da sauran ƙauyukan da ke makwabtaka da ita.
Wannan sabon harin ya zo ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin barazanar tsaro a Ƙaramar Hukumar Kebbe, inda rahotanni suka ce wasu al’ummomi da dama sun fuskanci hare-haren ‘yan bindiga, satar dabbobi da kuma raba mutane da muhallansu a cikin ‘yan makonnin nan.
Majiyoyin yankin sun kuma ce wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da shanu sama da 300 da rakuma bakwai daga Ungushi da ƙauyen Gwandi da ke makwabtaka da ita, yayin da wasu mazauna garuruwan suka tsere saboda tsoron hare-hare.
Wannan lamari ya faru ne kwanaki kaɗan bayan rahotannin wani babban hari da ake zargin mambobin ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa ne suka kai a wasu sassan Kebbe.
Rundunar ‘Yansndan Jihar Sokoto ta tabbatar da faruwar lamarin a yankin, amma ta ce tana ci gaba da tattara bayanai kafin fitar da cikakken bayani.
Ƙarin taɓarɓarewar tsaro a yankin ta sanya rundunar soji ƙara mayar da hankali kan Ƙaramar Hukumar Kebbe, inda Babban Kwamandan Runduna ta 8 ta Sojojin Nijeriya, Manjo Janar Bemgba Paul Koughna, ya ziyarci Sansanin Soji na Gaba-gaba (FOB) Kebbe ranar Lahadi domin duba halin tsaro da kuma shirye-shiryen dakarun domin yaki da sabbin barazanar da aka samu.
An ce ziyarar ta mayar da hankali ne kan tantance halin tsaro a zahiri da kuma ƙarfafa martanin sojoji ga barazanar da ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da ke aiki a yankin ke haifarwa.














