ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, July 27, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kuri’u Za Su Yi Tasiri A Zaɓen 2027, In Ji INEC

by Sulaiman
2 hours ago
Inec

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta kammala aikin rajistar masu kaɗa ƙuri’a (CVR) a faɗin ƙasar ranar Lahadi, gabanin babban zaɓen shekarar 2027, tare da buƙatar waɗanda suka yi rajista su jira lokacin da za a baje kundin sunayen masu zaɓe domin tantance bayanansu.

Hukumar ta kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa duk wata ƙuri’a ingantacciya da aka kaɗa za ta yi tasiri a zaɓukan da ke tafe.

INEC ta sanya ranar 26 ga Yulin 2026 a matsayin ranar ƙarshe ta aikin rajistar, wanda ya haɗa da sabbin rajista, sauya wurin rajista, gyaran bayanan masu zaɓe da kuma maye gurbin katin zaɓe na dindindin (PVC) da ya ɓace ko ya lalace.

ADVERTISEMENT

A wani ɓangare kuma, Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa hukumar na ci gaba da jajircewa wajen gudanar da sahihin zaɓe, inda kowace ƙuri’a ingantacciya za ta kasance mai tasiri.

Da yake jawabi yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa tsohon Shugaban Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Zaman Lafiya na Ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), a Minna, Jihar Neja, Amupitan ya ce duk da ƙalubalen da hukumar ke fuskanta, za ta tabbatar da cewa ra’ayin masu zaɓe ne ya yi rinjaye.

LABARAI MASU NASABA

Sojojin Ruwa Sun Cafke Jirgin Ruwa Maƙare Da Ɗanyen Mai Na Sata

Arewa Ta Rasa Alƙiblarta – Dattawan Arewa

A nasa jawabin, Janar Abdulsalami ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su bai wa INEC cikakken goyon baya wajen gudanar da sahihin zaɓe, yana mai cewa ci gaba da amincewar jama’a da tsarin zaɓe na da matuƙar muhimmanci ga dorewar dimokuraɗiyyar ƙasar.

Inec
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Za Ta Ci Gaba Da Kare Ikon Mulkin Yankuna Da Hakkoki Da Moriyarta Ta Teku
  • Sulaiman
    Xi Jinping Ya Mika Sakon Murnar Cika Shekaru 61 Da Samun ‘Yancin Kai Ga Shugaban Maldives
  • Sulaiman
    Sin Ta Ayyana Shirin Ko-ta-kwana Na Samar Da Tallafin Gaggawa Ga Lardin Guangdong
  • Sulaiman
    Fina-finan Kasar Sin Suna Haskakawa Tare Da Samar Da Dimbin Kudaden Shiga A Zangon Nuna Fina-finai Na Lokacin Zafi Na Bana

MASU ALAKA

Inec
Manyan Labarai

Sojojin Ruwa Sun Cafke Jirgin Ruwa Maƙare Da Ɗanyen Mai Na Sata

July 26, 2026
Arewa Ta Rasa Alƙiblarta – Dattawan Arewa
Manyan Labarai

Arewa Ta Rasa Alƙiblarta – Dattawan Arewa

July 26, 2026
Gwamna Uba Sani Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Kyauta Ga Manoma 150,000  A Kaduna
Manyan Labarai

Gwamna Uba Sani Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Kyauta Ga Manoma 150,000 A Kaduna

July 26, 2026

LABARAI MASU NASABA

Rashin Tsaro Na Barazana Ga Zaben 2027 —Rahotanni

Kuri’u Za Su Yi Tasiri A Zaɓen 2027, In Ji INEC

July 27, 2026
Auto Draft

ADC Ta Buƙaci Tinubu Ya Bai Wa Waɗanda Aka Sace A Kaiama Da Borno Kulawa

July 27, 2026
Inec

Sojojin Ruwa Sun Cafke Jirgin Ruwa Maƙare Da Ɗanyen Mai Na Sata

July 26, 2026
Sin Za Ta Ci Gaba Da Kare Ikon Mulkin Yankuna Da Hakkoki Da Moriyarta Ta Teku

Sin Za Ta Ci Gaba Da Kare Ikon Mulkin Yankuna Da Hakkoki Da Moriyarta Ta Teku

July 26, 2026
Xi Jinping Ya Mika Sakon Murnar Cika Shekaru 61 Da Samun ‘Yancin Kai Ga Shugaban Maldives

Xi Jinping Ya Mika Sakon Murnar Cika Shekaru 61 Da Samun ‘Yancin Kai Ga Shugaban Maldives

July 26, 2026
Inec

Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Naɗa Sabon Mai Ba Shi Shawara

July 26, 2026
Sin Ta Ayyana Shirin Ko-ta-kwana Na Samar Da Tallafin Gaggawa Ga Lardin Guangdong

Sin Ta Ayyana Shirin Ko-ta-kwana Na Samar Da Tallafin Gaggawa Ga Lardin Guangdong

July 26, 2026
Fina-finan Kasar Sin Suna Haskakawa Tare Da Samar Da Dimbin Kudaden Shiga A Zangon Nuna Fina-finai Na Lokacin Zafi Na Bana

Fina-finan Kasar Sin Suna Haskakawa Tare Da Samar Da Dimbin Kudaden Shiga A Zangon Nuna Fina-finai Na Lokacin Zafi Na Bana

July 26, 2026
Shugaban Senegal Ya Jinjinawa Kasar Sin Bisa Taimakon Gina Zaurukan Gudanar Da Wasannin Gasar Olympics Ta Matasa

Shugaban Senegal Ya Jinjinawa Kasar Sin Bisa Taimakon Gina Zaurukan Gudanar Da Wasannin Gasar Olympics Ta Matasa

July 26, 2026
Inec

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Alƙalin Babbar Kotu A Kebbi

July 26, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.