ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, June 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hukumar Shari’a Ta Kano Ta Hukunta Alƙalai Da Ma’aikata Kan Laifukan Rashin Ɗa’a

by Sulaiman
2 months ago

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano

Kotu Ta Ɗege Shari’ar Ganduje Da Wasu Mutum 7 Zuwa 14 Ga Oktoba 2026

Hukumar Kula da Ayyukan Shari’a ta Jihar Kano, ta ɗauki matakan ladabtarwa kan wasu jami’an shari’a da ma’aikata bisa laifukan rashin da’a, tana mai jaddada kudurinta na tabbatar da “tsari, gaskiya da riƙon amana a cikin ɓangaren shari’a.”

An cimma waɗannan matsayai ne a taro na 89 na hukumar da aka gudanar a ranar 16 ga Afrilu, 2026, kamar yadda kakakin hukumar, Baba Jibo Ibrahim, ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.Ibrahim ya ce hukumar ta amince da shawarwarin Kwamitin Karɓar Korafe-korafe na Jama’a na Shari’a dangane da ƙorafe-ƙorafe daban-daban da aka bincika.

Daga cikin waɗanda abin ya shafa akwai Mahmud Ahmed, jami’in sufuri na Babbar Kotun Kano, wanda aka samu da aikata abubuwan da suka wuce aikinsa, yin barazana ga jama’a, da amfani da sunan ɓangaren shari’a wajen tsoratar da mutane. An ba shi gargaɗi mai tsanani tare da umarnin ya takaita kansa ga aikinsa kawai.

A wani lamari, Mallam Salisu Buhari Mandawari, alƙalin Kotun Shari’ar Musulunci ta Ƙoli a Rogo, an same shi da aikata abubuwan da suka haɗa da nema da karɓar cin hanci, da kuma kasa rubuta bayanan shari’a yadda ya kamata. Hukumar ta rage masa matsayi da darajoji biyu, tare da dakatar da shi daga aikin shari’a na akalla shekaru uku, sannan zai riƙa karɓar rabin albashi.

Haka kuma, Alkali Umar Sunusi Danbaba na Kotun Shari’ar Musulunci ta Filin Hoki, an hukunta shi bayan an same shi da son zuciya, rashin rubuta bayanan shari’a yadda ya kamata, da kuma rashin kyakkyawan kula da kuɗi. Sabida haka, an dakatar da shi daga aikin shari’a na akalla shekaru uku, tare da karɓar rabin albashi na shekara guda.

Hukumar ta kuma gano cewa, Abdulbari Ado (Magatakardan Kuɗi) da Umar Abdulhamid (Magatakardan Gudanarwa) suna da hannu wajen karɓar cin hanci a wani lamari da ya shafi Kotun Shari’ar Musulunci a Rogo. Dukkaninsu an rage musu matsayi da darajoji biyu, an sanya su kan rabin albashi na shekara guda, tare da gargadin su da su guji sake aikata laifi.

A wani lamari daban, Sabiu Adam Inusa, Magatakardan Kuɗi a Kotun Shari’ar Musulunci ta Gwarzo, an same shi da bayar da rasit mai kura-kurai. Duk da an ɗauki lamarin a matsayin kuskure, hukumar ta ba shi gargaɗi tare da cire shi daga muƙaminsa na Magatakardan Kuɗi.

Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara
  • Sulaiman
    Salon Jagorancin Kasar Sin Na Ingiza Samar Da Ci Gaba Mai Nagarta
  • Sulaiman
    Dangote Ya Rage Farashin Fetur Zuwa N1,125 Kan Kowace Lita
  • Sulaiman
    Adadin Injunan Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ya Wuce Kilowatts Awa Biliyan 4, Wato Ya Kai Ga Matsayi Na Farko A Duniya
ADVERTISEMENT

MASU ALAKA

Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano
Manyan Labarai

Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano

June 25, 2026
Kotu Ta Ɗege Shari’ar Ganduje Da Wasu Mutum 7 Zuwa 14 Ga Oktoba 2026
Manyan Labarai

Kotu Ta Ɗege Shari’ar Ganduje Da Wasu Mutum 7 Zuwa 14 Ga Oktoba 2026

June 25, 2026
Ndume Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Yake Goyon Bayan Ƙudirin Kafa ‘Yansandan Jihohi
Manyan Labarai

Ndume Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Yake Goyon Bayan Ƙudirin Kafa ‘Yansandan Jihohi

June 25, 2026
Next Post
Aikin Maɗaciya A Jikin Ɗan’adam

Aikin Maɗaciya A Jikin Ɗan’adam

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

June 25, 2026
Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji

Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji

June 25, 2026
Shugabar Namibia Ta Kaddamar Da Dakin Baje Kolin Kimiyya Da Sinawa Suka Gina

Shugabar Namibia Ta Kaddamar Da Dakin Baje Kolin Kimiyya Da Sinawa Suka Gina

June 25, 2026
Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara

June 25, 2026
Salon Jagorancin Kasar Sin Na Ingiza Samar Da Ci Gaba Mai Nagarta

Salon Jagorancin Kasar Sin Na Ingiza Samar Da Ci Gaba Mai Nagarta

June 25, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Dangote Ya Rage Farashin Fetur Zuwa N1,125 Kan Kowace Lita

June 25, 2026
Adadin Injunan Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ya Wuce Kilowatts Awa Biliyan 4, Wato Ya Kai Ga Matsayi Na Farko A Duniya

Adadin Injunan Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ya Wuce Kilowatts Awa Biliyan 4, Wato Ya Kai Ga Matsayi Na Farko A Duniya

June 25, 2026
Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano

Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano

June 25, 2026
Wani Gidan Adana Kayan Tarihi Na Sin Ya Fitar Da Rahoton Yadda Dakarun Japan Suka Rika Zubawa Mutane Jinin Dabbobi Yayin Yakin Duniya Na Biyu

Wani Gidan Adana Kayan Tarihi Na Sin Ya Fitar Da Rahoton Yadda Dakarun Japan Suka Rika Zubawa Mutane Jinin Dabbobi Yayin Yakin Duniya Na Biyu

June 25, 2026
Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Bude Mashigin Hormuz

Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Bude Mashigin Hormuz

June 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.