Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta gayyaci mawaki Tijjani Gandu kan zargin karya dokokinta da ya shafi wata sabuwar waƙa da ya fitar.
Hukumar ta ce dole ne mawaƙa, marubuta da sauransu, su gabatar da ayyukansu domin a duba su kuma a amince da su kafin su fitar da su ga jama’a.
A cewar hukumar, ana yin wannan duba ne domin tabbatar da cewa abubuwan da aka samar ba su ƙunshi kalmomi ko saƙonnin da za su iya haifar da rikici a tsakanin jama’a ko barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali ba.
Hukumar ta gargaɗi Gandu cewa rashin amsa gayyatar na iya jawo masa fushin doka.
Tijjani Gandu, mawaƙi ne a Kano da ke yin tafiyar siyasa ta ƙungiyar Kwankwasiyya.
Ya taɓa riƙe muƙamin mai bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf shawara kan al’adu da nishaɗi.
Hukumar ta buƙaci Gandu da sauran masu fasaha da su ci gaba da bin dokokinta.













