Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta gargaɗi al’ummar Nijeriya game da wani shafin yanar gizo na bogi da ke yawo a dandalin sada zumunta, wanda ke iƙirarin cewa an buɗe rajistar masu kaɗa ƙuri’a ta intanet domin zaɓukan gaba.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa ba ta da wata alaƙa da wannan shafi, tana mai jaddada cewa shiri ne na yaudara da wasu ɓata-gari suka ƙirƙira da nufin damfarar ƴan ƙasa da kuma sace bayanan sirrinsu ta hanyar intanet.
Hukumar ta fayyace cewa a duk lokacin da aka shirya fara aikin sabunta rajistar masu zaɓe (CVR), za ta sanar da al’umma a hukumance ta hanyar kafofin yaɗa labarai na gaskiya da kuma shafukanta na asali, ba wai ta hanyar hanyoyin yanar gizo (links) da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.
Haka kuma, INEC ta buƙaci ƴan Nijeriya da su kasance masu sanya idanu tare da guje wa shiga irin waɗannan shafuka ko bayar da muhimman bayanansu na sirri, kamar lambar zama ɗan ƙasa (NIN), da lambobin waya, ko bayanan banki domin kare kansu daga faɗawa tarkon masu zamba ta intanet.
Hukumar zaɓen ta bayyana cewa tana aiki tare da jami’an tsaro da hukumomin da ke kula da harkokin yaƙi da laifukan intanet domin gano waɗanda ke da hannu a ƙirƙirar wannan shafin bogi domin a ɗauki matakin doka a kansu.














