Dakarun Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, ‘Operation FANSAN YAMMA’, sun kuɓutar da fasinjoji 33 da wasu ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a yankin Magazu da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.
An samu nasarar kuɓutar da mutanen ne a daren Asabar, 8 ga Agusta, 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri da kuma gaggawar ɗaukar mataki daga dakarun Shiyya 2 na Rundunar Haɗin Gwiwar, tare da haɗin gwiwar jami’an Rundunar ‘Yansandan Nijeriya (NPF) da aka jibge a Tsafe.
Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar Haɗin Gwiwar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi.
A cewarsa, dakarun sun samu bayanan cewa wasu ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da matafiya da ke wucewa ta yankin Magazu.
Ya ce nan take dakarun suka shirya suka nufi yankin, inda suka yi arangama da ‘yan ta’addan da suke kan hanyar kai waɗanda aka yi garkuwa da su zuwa wata maɓoyarsu.
Danja ya ce da ‘yan ta’addan suka hango dakarun, sai suka buɗe musu wuta, amma sojojin suka mayar da martani da ƙarfi, lamarin da ya tilasta wa maharan barin mutanen da suka yi garkuwa da su tare da tserewa zuwa cikin dazuzzukan da ke kusa.
Ya ce an samu nasarar kuɓutar da dukkan mutane 33 ba tare da wani rauni ba.














