ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jami’an Tsaro Sun Yi Arangama Da Ƴan Bindiga 240 A Kan Iyakar Zamfara Da Kebbi

by Abubakar Sulaiman
1 month ago

Jami’an tsaron sun yi wata fafatawa mai zafi da wani gungun miyagun ƴan bindiga da yawansu ya kai kusan 240 a yankin kan iyakokin Jihohin Zamfara da Kebbi, a ranar Litinin, 10 ga watan Agusta, 2026, domin daƙile yunƙurinsu na cin karensu babu babbaka a yankin.

Kamar yadda bayanan da aka tattara suka tabbatar, ƴan bindigar sun ɓullo ne daga wata maɓoya da ake kira Sangeko Gap a Jihar Zamfara, inda suka nufi garin Makuku da ke cikin Jihar Kebbi. Nan take dakarun sojoji na Bataliya ta 3 (COAS Intervention Battalion 3) ƙarƙashin Divishin na 8, tare da dakarun sojin sama na Operation FANSAR YAMMA da jami’an ƴansanda makwantar da tarzoma (Mobile Police Force) suka tari gabansu da luguden wuta.

Wani ganau mai suna Fua’ad Bello ya bayyana cewa maharan sun rabu gida uku ne a lokacin da suke gudanar da wannan ta’addanci. Wannan mummunan yanayi ya sanya mazauna garuruwan da ke kewaye shiga cikin mawuyacin hali, inda tuni jama’a suka fara ficewa daga muhallansu zuwa yankunan da ke da ɗan dama-dama domin neman mafaka yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da ruwan harsasai.

ADVERTISEMENT

Wani jami’in ɗansanda da ke aiki a yankin ya tabbatar da cewa babbar manufar tura waɗannan dakarun haɗin gwiwa ita ce don hana ƴan bindigar samun gindin zama ko shiga wasu ƙauyukan da ke kusa su aika ta ɓarna. Ya kuma buƙaci al’ummar yankin da su ci gaba da kasancewa cikin taka-tsantsan tare da bin umarnin jami’an tsaro har sai an kammala aikin kakkaɓe maharan gaba ɗaya.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto a yammacin ranar 10 ga watan Agusta, 2026, hukumomin tsaro ba su su fitar da wata ƙididdiga ta hukuma ba dangane da adadin waɗanda suka rasa rayukansu ko suka raunata daga ɓangarorin biyu ba.

LABARAI MASU NASABA

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku
  • Abubakar Sulaiman
    An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro
  • Abubakar Sulaiman
    Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18
  • Abubakar Sulaiman
    Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

MASU ALAKA

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku
Labarai

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

September 12, 2026
An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro
Labarai

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

September 12, 2026
Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18
Labarai

Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

September 12, 2026
Next Post
An Bude Kafar Rejistar Halartar Baje Kolin CIFTIS Na 2016 Ga Manema Labarai

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Sanata Yari Ya Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

September 12, 2026
Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

September 12, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa

September 12, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?

September 12, 2026
Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.