ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jihar Kogi Ta Ƙwace Ɗimbin Makamai, Ta Daƙile Shirin Kai Harin Ramuwar Gayya

by Sulaiman
2 months ago
Kogi

Gwamnatin Jihar Kogi ta sanar da cewa wani gagarumin samamen tsaro da aka gudanar ya kai ga ƙwace ɗimbin makamai da harsasai, waɗanda aka ce an nufi miƙa su ne ga wasu miyagun mutane da ke neman gurgunta zaman lafiya da tsaron jihar.

Wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa na Jihar, Kingsley Femi Fanwo, ya fitar ranar Litinin, ya bayyana cewa wannan nasara ta samu ne sakamakon haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaron cikin gida ƙarƙashin tsarin tsaro na Jihar Kogi, dakarun haɗin gwiwa (Hybrid Forces) da ke aiki ƙarƙashin Ofishin Mai Ba Gwamnati Shawara kan Tsaron Ƙasa (ONSA), da kuma Runduna ta 12 na Gidan Sojan Nijeriya, bayan sun yi aiki bisa sahihan bayanan sirri.

Fanwo ya bayyana cewa: “Bayanai na farko sun nuna cewa jami’an tsaro sun sami bayanan sirri kan zirga-zirgar makamai da harsasai da aka yi niyyar kai wa wasu ɓata-gari da ke gudanar da ayyukan laifi a ciki da kewayen Jihar Kogi.”

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Bayanan sirrin sun fito fili sun gano wata mota ƙirar Golf 2 da ake amfani da ita wajen gudanar da wannan safarar makamai ta haramtacciyar hanya.”

“Bayan samun bayanan sirrin cikin hanzari, hukumomin tsaro sun daidaita ayyukansu a faɗin iyakokin jihohi, kuma tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Sokoto da hukumomin tsaro na jihar, sun yi nasarar bin diddigin zirga-zirgar waɗanda ake zargi da motarsu yayin da suke ci gaba da sanya musu ido na kusa.”

LABARAI MASU NASABA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari

“Wannan samame ya kai ga kama mutum uku da ake zargi a Jihar Sokoto bayan da aka sanya musu idon sirri (coɓert surɓeillance) na tsayin fiye da makonni biyu. Binciken farko ya samar da muhimman bayanan sirri, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kamo sauran mambobin ƙungiyar masu safarar makaman da ke neman rura wutar laifuka a Jihar Kogi.”

“Bisa ga bayanan sirrin da aka samu ta hanyar wannan samame, jami’an tsaro sun yi nasarar tarewa tare da ƙwace ɗimbin makamai da harsasai da aka yi niyyar kai wa miyagun mutane a Jihar Kogi.”

“Daga bisani kuma, an cafke motar Golf 2 da aka yi amfani da ita wajen safarar makaman ta haramtacciyar hanya a garin Kabba, da ke cikin Ƙaramar Hukumar Kabba-Bunu.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Abubuwan da aka ƙwato a yayin wannan samame sun haɗa da bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, rumbun adana harsasai (magazines) na AK-47 da dama, harsasai masu rai na 7.62mm guda sittin da bakwai (67), gajerun bindigogi guda biyu, harsasan gajeriyar bindiga guda goma sha biyu (12), da kuma kayan sarki na soja (military uniforms) waɗanda ake zargin an yi niyyar bai wa miyagun mutane domin amfani da su a ayyukansu na ta’addanci.”

“Rahoton sirri ya nuna cewa makaman da aka tare ɗin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ɓata-gari ke yi na sake cika rumbun makamansu da suka kare, bayan da suka fuskanci gagarumin koma-baya a ayyukansu a makonnin baya-bayan nan, musamman ma biyo bayan karkashe shahararren shugaban ƴan fashi nan, Kachalla Battijo, a ranar 10 ga watan Yuni, 2026, bayan gazawar yunƙurinsa na sace ɗaliban Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Iluke Bunu.”

“Sakamakon hasashen yiwuwar kai harin ramuwar gayya da kuma yunƙurin fito-na-fito da miyagun da ke tserewa ke yi na sake haɗuwa da neman makamai, nan take Gwamnatin Jihar Kogi ta tsananta ƙoƙarin tattara bayanan sirri, ta faɗaɗa ƙofofin bincikenta, ta ƙarfafa sanya ido a wurare masu muhimmanci, sannan ta zurfafa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro a faɗin ƙasar nan domin tabbatar da cewa an gano tare da murƙushe duk wani shiri makamancin haka kafin a aiwatar da shi.”

“Bayanan sirri da ke ga gwamnatin jihar sun nuna cewa ragowar miyagun da suka maƙale a cikin dazuzzuka a sassan jihar sun fuskanci gagarumar naƙasu a ayyukansu, kuma suna fama da matsanancin ƙarancin makamai da harsasai biyo bayan ɗorewar samamen tsaro da ake kai musu.”

Bayanan sirrin da ake da su sun ƙara nuna cewa waɗannan matsanantan mambobi suna ta faɗi-tashi wajen ganin sun sake cika rumbun makamansu a yunƙurin yaki na fitar da kansu daga matsin lamba na tsaro da dakarun tsaro ke yi musu ba ƙaƙƙautawa.

Gwamnatin Jihar Kogi, bayan da ta yi hasashen irin waɗannan matakai tun da farko, ta riga miyagun zama ta hanyar faɗaɗa tsarin sadarwar ta na sirri, ƙarfafa ayyukan sanya ido, da kuma yin aiki kafaɗa-da-kafaɗa da hukumomin tsaro domin daƙile zirga-zirgar makamai da sauran kayayyakin masarufi da aka yi niyyar kai wa ɓata-garin.

“Nasarar tare wannan kaya na makamai wata bayyanar shaida ce da ke nuna cewa Gwamnati tana gaba da matakai da dama a kan waɗanda ke neman barazana ga zaman lafiyar jihar.”

Kogi
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030
  • Sulaiman
    Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari
  • Sulaiman
    Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya
  • Sulaiman
    Ɗabi’un Annabi (SAW) Kan Abubuwa Na Al’adar Rayuwa

MASU ALAKA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro
Manyan Labarai

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 11, 2026
Sanata yari
Labarai

Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari

September 11, 2026
Kogi
Labarai

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Next Post
Sin Ta Yi Kiran Bin Ka’idojin Takunkumin Makamai Da Kwamitin Sulhun MDD Ya Kakaba Wa Kungiyoyi Masu Dauke Da Makamai A DRC

Sin Ta Yi Kiran Bin Ka'idojin Takunkumin Makamai Da Kwamitin Sulhun MDD Ya Kakaba Wa Kungiyoyi Masu Dauke Da Makamai A DRC

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

September 11, 2026
Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 11, 2026
Sanata yari

Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari

September 11, 2026
Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

September 11, 2026
SAW

Ɗabi’un Annabi (SAW) Kan Abubuwa Na Al’adar Rayuwa

September 11, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000

Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000

September 11, 2026
Kogi

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

September 11, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026
Kogi

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.