Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, ta ce daga watan Janairu zuwa watan Yunin bana, jimilar darajar hada-hadar shige da fice a fannin bayar da hidimomi ta Sin, ta haura yuan tiriliyan 3.7, adadin da ya karu da kashi 8.3%, kan na makamancin lokaci na bara, inda yanayin cinikin fannin ya nuna wasu alamu kamar haka:
Na farko, cinikayyar dake bukatar hidimar ilimi ko kwarewa, ta kai fiye da rabin jimilar darajar hada-hadar shige da fice, a ciki kuma, fitar da kayayyakin da suka shafi al’adu da nishadi, da kuma ikon mallakar ilimi sun karu cikin sauri, inda saurin karuwarsu ya kai kashi 57.2% da 44.3% bi da bi.Na biyu kuma, fitar da kayayyakin da suka shafi bayar da hidimar yawon bude ido, da shigo da kayayyakin da suka shafi bayar da hidimar sufuri sun karu cikin sauri, inda suka karu da 31.1% da 30.4% bi da bi, daga watan Janairu zuwa Yunin bana. (Safiyah Ma)














