Jam’iyyar ADC ta buƙaci Majalisar Wakilai ta sake duba ƙudirin gyaran kundin tsarin mulki na kafa ‘yansandan jihohi.
Jam’iyyar ta ce ya kamata a sake bi ta hanyar da ta dace kuma a buɗe ta ga jama’a, bayan rahotannin da ke cewa an ƙirga wasu ƙuri’un ‘yan majalisa ta manhajar WhatsApp, tare da ƙirga wasu da ba sa cikin zauren majalisar lokacin kaɗa ƙuri’a.
ADC ta ce tana goyon bayan kafa ‘yansandan jihohi, amma dole ne a bi tanadin kundin tsarin mulki wajen yin gyaransa.
Ta kuma bayyana cewa ba a bai wa ‘yan Nijeriya damar tattaunawa kan ƙudirin ba.
Jam’iyyar ta buƙaci Majalisar Wakilai ta mayar da ƙudirin domin a sake tattauna shi a fili tare da bai wa jama’a damar bayyana ra’ayoyinsu, domin tabbatar da cewa zai magance matsalolin tsaro ba tare da tauye doka ba.














