Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) ta kashe wani babban kwamandan ƙungiyar ISWAP, Abu Khalid Al Muhajir, tare da wasu mayaƙa takwas, a wani hari ta sama da aka kai kan maɓoyar ‘yan ta’addan a Jihar Borno.
An bayyana Khalid Al Muhajir a matsayin wani fitaccen kwamandan ISWAP wanda ke da alhakin samar da tsaro na musamman domin rakiyar manyan shugabannin ƙungiyar ta’addancin.
Kakakin Rundunar Sojin Sama, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa harin ya kashe manyan shugabannin ISWAP guda tara, ciki har da wani babban kwamanda da ake zargin yana da alhakin taimaka wa manyan ‘yan ƙungiyar wajen zirga-zirga da kare lafiyarsu.
Ya ce an gudanar da aikin ne ranar Asabar, 8 ga Agusta, 2026, bayan rundunar ta samu sahihan bayanan sirri kan ayyuka da kuma zirga-zirgar wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne a yankin dajin Sambisa.
A cewarsa, bisa bayanan da aka samu, NAF ta tura wani jirgi mara matuƙi domin ci gaba da gudanar da aikin leƙen asiri, sa ido da bincike, wanda ya taimaka wajen ganowa tare da bin diddigin wasu ‘yan ta’adda yayin da suke tafiya zuwa wata maɓoya da ake zargi.
Ya ƙara da cewa bayan tabbatar da ainihin wurin da ‘yan ta’addan ke ɓuya, jirgin saman NAF ya kai hari inda ya tarwatsa maɓoyar.
A cewar rundunar, binciken da aka gudanar bayan harin ya nuna cewa an yi wa maɓoyar ‘yan ta’addan mummunar illa, inda aka samu nasarar kashe wasu daga cikin ‘yan ta’addan.
Air Commodore Ehimen ya ce ƙarin bayanan sirri da aka samu bayan harin sun tabbatar da cewa mayaƙan ISWAP tara sun mutu, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.














