ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kafafen Labaru Na Duniya Sun Bada Shawarar Sake Tunani Kan Alfanun Raya Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya

by Sulaiman
4 months ago

LABARAI MASU NASABA

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Yayin da rikicin Amurka da Isra’ila da Iran ya kara haifar da barazanar tsaro da ke tattare da tsoffin hanyoyin jiragen ruwa, wasu kafafen yada labaru na sassan kasa da kasa, ciki har da jaridar Daily Mirror ta kasar Sri Lanka, da kafar labarai ta shafin intanet mai suna Observatorio de la Política China ta kasar Sifaniya, sun yaba da tashoshin jiragen ruwa da kamfanonin kasar Sin suka gina, da zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin kasar Sin da Turai, inda suka bada shawarar sake yin tunani kan alfanu gami da ma’anar raya shawarar Ziri Daya da Hanya Daya cikin hadin gwiwa, wadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bullo da ita.

Jaridar Daily Mirror ta ruwaito cewa, yawaitar rikicin yankin Gabas ta Tsakiya ta taimaka ga ci gaban harkokin tashar jiragen ruwa ta kasa da kasa ta Hambantota da ke kudancin kasar Sri Lanka, tashar da ta kasance wani muhimmin aikin hadin gwiwar Sin da Sri Lanka a bangaren raya shawarar Ziri Daya da Hanya Daya.

Tsakanin watan Janairu zuwa Maris din bana, yawan hajojin da aka shigo gami da fitar da su tashar, ya zarce tan miliyan 2.01, adadin da ya karu da kaso 47 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.Tun bayan da shugaba Xi Jinping ya bullo da ra’ayin raya shawarar Ziri Daya da Hanya Daya cikin hadin gwiwa a shekara ta 2013, ya zuwa yanzu, shawarar ta riga ta karade kasashe sama da 150 da kungiyoyin kasa da kasa sama da 30.

ADVERTISEMENT

Ita kuwa kafar labarai ta shafin intanet ta Observatorio de la Política China ta kasar Sifaniya ta wallafa wani bayani ne da ke cewa, raya shawarar Ziri Daya da Hanya Daya cikin hadin gwiwa, ya sauya ajandar kasar Sin bisa manyan tsare-tsare zuwa babban tsarin hadin gwiwa mai kunshe da muhimman ababen more rayuwa, da kara mu’amalar mabambantan sassa, da cinikayya da kere-kere da sauransu, al’amarin da ya zama babban karfin dunkule shiyyar da ma duk duniya baki daya. (Murtala Zhang)

Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen
  • Sulaiman
    Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
  • Sulaiman
    Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

MASU ALAKA

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen
Daga Birnin Sin

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026

September 9, 2026
Next Post
inec

Kotun Abuja Ta Hana INEC Amincewa Da Tarukan ADC

LABARAI MASU NASABA

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.