Hukumar Kare Hakkin Masu Amfani da Kayayyaki ta Jihar Kano (KCPC) ta karɓi kayan amfanin yau da kullum da wa’adin amfaninsa ke dab da karewa, wadanda kudinsu ya kai Naira miliyan 28,615,200 daga Kamfanin SUFAYE Investment, inda ta mika kayan da kanta domin hana su shiga kasuwannin jihar.
Da yake karɓar kayayyakin, Sakataren Zartarwa na KCPC, Dakta Ibrahim Garba Muhammad, ya yaba wa shugabancin kamfanin bisa fifita lafiyar al’umma da kare lafiyar masu amfani da kayayyaki fiye da neman riba.
Dakta Muhammad ya bayyana matakin da kamfanin ya dauka a matsayin alamar kishin kasa, gaskiya da rikon amana, tare da cewa hakan ya yi daidai da babban aikin majalisar na kare al’umma daga amfani da kayayyakin da ba su da aminci.
Ya yaba wa SUFAYE Investment bisa kiyaye ka’idojin gudanar da kasuwanci cikin gaskiya, musamman yadda ta mika kayayyakin maimakon barin su shiga kasuwa tare da jefa lafiyar masu amfani da su cikin hadari.
Shugaban hukumar kuma ya bukaci sauran ‘yan kasuwa da kamfanoni a fadin Jihar Kano da su yi koyi da wannan mataki, ta hanyar cire kayayyakin da suka lalace, da wadanda wa’adin amfani su ya kare daga wuraren sayarwa.
Dakta Muhammad ya tabbatar wa jama’a cewa, gwamnatin Jihar Kano za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace wajen sanya ido da daidaita harkokin kasuwanni, tare da godiya ga al’ummar jihar da ‘yan kasuwa masu bin ka’ida bisa taimakawa ayyukan sa ido na hukumar.














