Rundunar ‘Yansandan Jihar Sokoto ta ce ta hallaka wasu mutane biyu da ake zargi ‘yan bindiga ne tare da kama wasu mutane 11 a wasu samame daban-daban da ta gudanar domin dakile ayyukan ‘yan bindiga, satar babura da sauran laifuka a fadin jihar.
Rundunar ta kuma kwato bindigogin AK-47 guda biyu, harsasai 54, mujallu, bindiga kirar gida guda daya da kuma babura 14 da aka sace yayin ayyukan da aka gudanar tsakanin ranakun 14 da 15 ga Agusta, 2026.
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yansandan jihar, DSP Ahmad Rufa’i, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya ce daga cikin ayyukan akwai nasarar dakile wani yunkurin harin ‘yan bindiga da suka kai kauyen Dankadu da ke Karamar Hukumar Illela.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar.
Don haka, Kwamishinan ya bukaci mazauna jihar da su kasance cikin taka-tsantsan tare da gaggauta sanar da ‘yansanda duk wani motsi ko abin da suke zargin abu ne mai barazana.
Ya kuma gargadi jama’a da su guji sayen baburan da aka sace, yana mai cewa duk wanda aka samu yana saye ko hulda da kadarorin sata zai fuskanci hukunci a gaban doka.














