A Babban Asibitin Katsina, wani ma’aikacin lafiya yana danna ma’aunin nauyi na inji, wanda aka ajiye kusa da jerin buhunan Abincin Maganin Cutar Tamowa da Aka Shirya Amfani da Shi (RUTF), alluran rigakafi da kuma tef din (MUAC).
Wannan wuri shi ne cibiyar wata babbar shirin inganta lafiyar yara: hadin gwiwar samar da abinci mai gina jiki na Naira miliyan 200 tsakanin Gwamnatin Jihar Katsina da UNICEF, wanda aka fadada tare da wani gagarumin shirin yi wa yara rigakafi a fadin jihar.
Yayin da takardun manufofin gwamnati ke takaita wannan hadin gwiwa ta fuskar kasafin kudi da manufofin kididdiga, ainihin tasirinsa na bayyana ne a cikin al’umma, inda ake auna nasarar shirin ta hanyar rayukan da aka ceto da kuma yaran da ke murmurewa daga rashin lafiya.
Iyaye mata da ke zuwa asibitin suna ba da labaran irin kalubalen da suka fuskanta a rayuwarsu, inda suka gamu da mummunar tamowa, cututtukan da za a iya ba da kariya a kansu, da kuma rashin samun alluran rigakafi kafin a fadada ayyukan lafiya ga jama’ar yankunansu.
Adnan, yaro ne dan wata 18, yana zaune cikin natsuwa a cinyar mahaifiyarsa Amina. Makonni shida da suka gabata, jikinsa ya yi rauni, yana fama da zazzabi, kuma nauyinsa na raguwa cikin sauri.
Amina ta ce: “Ya daina wasa kuma ya ki cin abinci. Hannuwansa sun koma sirara kamar sanduna, idonunsa sun fara canza launi zuwa fari. Na yi tunanin zan rasa shi.”
Kazalika wata mahaifiyar kuma tana rike da ’yarta Zainab mai watanni 8, wadda ta shafe watanni tana fama da yawan gudawa da cushewar kirji. Saboda aikin gona na yanayi da kuma rashin zuwa asibitin unguwa, Zainab ta rasa dukkan alluran rigakafin yara da ya kamata a yi mata.
Mahaifiyar ta ce: “Kowane mako biyu tana rashin lafiya, kuma mun kashe ‘yan kudaden da muke da su wajen yin magungunan gargajiya a gida, amma ba su taba taimaka mata ba.”
Ziyararmu ta zo daidai da kaddamar da rajistar masu cin gajiyar shirin 184,105 karkashin Asusun Samar da Kiwon Lafiya a Matakin Farko (BHCPF) 2.0, wanda Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya kaddamar a Babban Asibitin Katsina.
Hukumar Kula da Tsarin Inshorar Lafiya a Jihar Katsina (KTSCHMA) ce ta tsara shirin, wanda ke da nufin tallafa wa mazauna yankin da ke cikin yanayi na rauni a dukkan kananan hukumomi 34 da kuma mazabu 361 na jihar.
Masu ruwa da tsaki sun ce jihar da alama tana amfani da shirye-shirye daban-daban domin magance kalubalen da ke fuskantar samar da kiwon lafiya. A Karamar Hukumar Charanchi, an ga mata sanye da hijabai masu launuka daban-daban suna taruwa a wajen Cibiyar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Charanchi.
Daya daga cikinsu, Hauwa, ta zo da danta Kabir mai shekaru biyu, wanda rashin lafiyarsa ta yi tsanani har kafafunsa sun fara kumbura saboda taruwar ruwa a jiki (edema).
“Ya kasa tsayawa da kafafunsa. Makwabtanmu sun gaya mana cewa matsalar ta shafi al’amuran numfashi ne, amma da muka kawo shi nan, ma’aikatan lafiya suka nuna mana cewa yunwa da rashin isassun sinadarai masu gina jiki ne suka jawo masa matsalar.”
Mariam ma ta zo da Usman dan wata shida domin a yi masa allurar rigakafin kyanda da kuma ta shan Inna ta baki. Ta kuduri aniyar ba za ta sake maimaita abin da ya faru a baya ba.
Ta ce kanwarta ta rasa danta na fari shekaru da suka gabata sakamakon zazzabi mai tsanani, saboda babu allurar rigakafi a kusa da su. Don haka, tana son tabbatar da cewa an kare danta tun daga farko.
A Katsina da Charanchi, da sauran cibiyoyin kiwon lafiya da ke fadin jihar, iyalai na samun cikakkiyar kulawar lafiya wanda ke taimakawa wajen sauya yanayin lafiyar ’ya’yansu kai tsaye.
Ma’aikatan lafiya sun ce lokacin da aka fara auna Adnan da tef din MUAC mai launuka daban-daban, hannunsa yana cikin launin ja, wanda ke nuna cewa yana fama da tsananin karancin abinci mai gina jiki.
Ma’aikatan lafiya sun shigar da shi cikin shirin kula da masu fama da tamowa ba tare da kwanciya a asibiti ba, inda aka rika ba shi man gyada mai dauke da sinadarai masu gina jiki da kuzari mai yawa, wato RUTF kullum a mako, tare da ba mahaifiyarsa shawarwari kan yadda za ta ciyar da jaririn.
“Cikin makonni uku da fara cin wannan man, Adnan ya fara murmushi. Yanzu tef din da ake auna hannunsa yana cikin launin kore, kuma yana ta wasanninsa a harabar gida,” in ji mahaifiyarsa.
Wasu yara, kamar Zainab, sun samu allurar rigakafin da suka rasa a baya, tare da gishirin ORS na mayar da ruwa a jiki da kuma karin sinadarin zinc. Usman ya samu allurar rigakafin da ya kamata a yi masa a lokacin da ya dace, tare da muhimmin karin sinadarin Bitamin A, yayin da wasu yaran suka samu kulawa ta musamman wadda ta magance kumburin jikinsu kafin a saka su cikin shirye-shiryen ciyar da masu fama da tamowa.
Wadannan labarai masu dadada rai ba su kawar da gaskiyar cewa samun kulawar lafiya abu ne da ke bukatar jajircewa a kullum ga iyaye mata da ke zaune a kauyuka masu nisa ba, domin an gaya mana cewa iyaye mata kan yi tafiyar kafa mai nisan kilomita takwas zuwa 15 domin zuwa cibiyoyin kiwon lafiya, inda tafiyar zuwa da dawowa kan dauki tsawon sa’o’i hudu zuwa takwas.
Ga wadanda ba za su iya yin wannan tafiya mai nisa da kafa ba, kudin babur na haya yana kai wa tsakanin Naira 1,000 zuwa 1,800, wanda ke da matukar tsada ga iyalai masu karamin karfi, domin kudin ya kusan kai wa na abincin yini guda.
“Domin in zo nan yau, sai da na bar gida da karfe 6:00 na safe, na yi tafiyar kafa kusan sa’o’i biyu ina dauke da Kabir. Idan na hau babur, kudin zai zama daga cikin kudin da za mu yi amfani da su wajen sayen abincin dare,” in ji Hauwa.
Duk da wadannan kalubalen na jiki da na tattalin arziki, dattawan al’umma da ma’aikatan lafiya na yankin sun bayyana cewa ana ganin sauyi mai kyau a yawan yaran da ke tsira da rayuwa a fadin jihar.
Usman Ibrahim, wani mai aikin sa-kai na lafiya a kauye, wanda ke ziyartar gidaje domin duba yara da kuma karfafa iyaye su kai su cibiyoyin kiwon lafiya, ya ce yana ganin sauyin kai tsaye a yayin ziyarar gidaje da yake yi a kullum.
Ya ce a ’yan shekarun da suka gabata, kusan kowanne wata ana jin labarin mutuwar yara a kauyen sakamakon matsananciyar rauni ko zazzabi.
“Yanzu, saboda muna gano tamowa tun da wuri ta amfani da tef din MUAC, sannan muna kai allurar rigakafi har kofar gidajensu a lokacin gangamin rigakafi, an samu raguwar wadannan mace-macen yara matuka,” in ji shi.
Yawancin iyaye mata da ke zaune a wuraren jiran aiki na cibiyoyin kiwon lafiya daban-daban a fadin jihar sun amince da abin da Usman ya ce, inda suka bayyana cewa ziyartar asibiti cikin gaggawa da kuma mace-macen yara sun ragu sosai a unguwanninsu.
Sai dai, duk da wadannan nasarori da ake gani a fili, har yanzu akwai manyan kalubalen gudanar da ayyuka, musamman ga iyalan da ke zaune a yankunan karkara masu nisa, inda yanayin kasa mai cike da koguna, karancin ma’aikatan lafiya, da yawan marasa lafiya da ke karashin kulawar ma’aikacin jinya guda daya ke ci gaba da kasancewa matsala.
Hafsat Bello, wadda ke kula da cibiyar lafiya ta PHC Charanchi, ta bayyana yadda aka samu ci gaba tare da kalubalen sufuri da gudanar da ayyuka da suke ci gaba da fuskanta a aikace.
“Karkashin wannan hadin gwiwa, yawan yaran da muke kula da su a halin yanzu ta shirin OTP ya ba mu damar samun nasarar yi wa yara sama da 850 da ke fama da matsananciyar tamowa magani tare da sallamar su cikin shekarar da ta gabata a wannan yankin da cibiyarmu ke kula da shi kadai,” in ji ta.
“Amma babban kalubalenmu shi ne tabbatar da wadatar kayan magani da kuma nisa. Idan ruwan sama mai karfi ya lalata hanyoyin karkara, ko kuma motocin da ke kawo kayan sun samu jinkiri, muna fuskantar karancin RUTF na dan lokaci.
“Idan uwa ta yi tafiyar kilomita 12 sannan ta iso ta tarar cewa kayan da muke da su sun kusa karewa, abin yana karya zuciya. Muna bukatar karin wuraren kai ayyukan lafiya na wucin gadi zuwa kananan yankuna, da kuma tabbatar da cewa kayan suna kasancewa a wadace a kodayaushe, domin mu iya kai wa kowane yaro da ke bukatar taimako,” in ji ta.
Hadin gwiwar gwamnatin jihar da UNICEF na Naira miliyan 200, tare da fadada gangamin rigakafi, ya nuna cewa tsare-tsaren da aka shirya musamman domin bukatun al’umma na iya ceton rayuka tun daga matakin kasa.
Ga iyaye mata, masu aikin sa-kai na lafiya a kauyuka da ma’aikatan lafiya a wurare kamar Charanchi, wannan shiri ya wuce zama wata manufar gwamnati kawai. A wurinsu, shi ne bambancin da ke tsakanin rasa yaro da kuma ganin yaron ya girma cikin koshin lafiya.
Tsawon shekaru, Jihar Katsina ta fuskanci manyan kalubalen kiwon lafiyar jama’a. Matsananciyar tamowa a matakin al’umma (GAM) ta jefa dubban yara ‘yan kasa da shekara biyar cikin hadari, yayin da gibin da ake samu wajen yin rigakafi ya bar al’ummomi da dama cikin hadarin kamuwa da cututtukan yara da za a iya dakile su.
Abin da ya fara a matsayin kudirin ware Naira miliyan 200 da aka mayar da hankali a kai, ya bunkasa zuwa wata babbar hadin gwiwa ta dabarun kiwon lafiya da ta kai daruruwan biliyoyin Naira. Ta hanyar mayar da hankali kai tsaye kan ayyukan da ke da matukar tasiri da kuma hanyoyin kai hidima a matakin al’umma, wannan hadin gwiwa na sauya alkaluman tsiran yara da kuma kare iyalai masu rauni a fadin jihar.
Ci gaba da rike wadannan nasarori da kuma fadada su zai dogara ne a karshe kan cike sauran gibin da ke cikin hanyoyin samar da kayayyaki, karancin ma’aikatan lafiya da kuma samun damar kai ayyukan lafiya zuwa yankunan karkara a fadin jihar.













