ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kano Pillars Ta Naɗa Mataimakin Kocin Super Eagles, Daniel Ogunmodede A Matsayin Sabon Kocinta

by Rabilu Sanusi Bena
2 months ago

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sanar da naɗa Daniel Ogunmodede, mataimakin kocin Super Eagles, a matsayin sabon kocin ƙungiyar domin jagorantarta a kakar wasa ta 2026/2027.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, inda ta ce ta cimma yarjejeniya da Ogunmodede kan jagorantar ƙungiyar.

Kafin wannan naɗi, ana ta hasashen wanda zai zama sabon kocin Kano Pillars gabanin fara sabuwar kakar wasa.

ADVERTISEMENT

Ogunmodede mai shekaru 46 ana sa ran zai sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyu.

Sabon kocin ya jagoranci a baya Remo Stars, inda ya jagoranci ƙungiyar ta lashe Gasar Firimiyar Nijeriya a kakar wasan 2024/2025.

LABARAI MASU NASABA

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Baya ga haka, yana cikin masu taimaka wa kocin Super Eagles, Eric Chelle, kuma ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin matasan masu horar da ƙwallon ƙafa mafi ƙwarewa a Nijeriya.

Magoya bayan Kano Pillars na fatan sabon kocin zai kawo sauyi tare da mayar da ƙungiyar kan turbar nasara bayan gaza yin kataɓus a kakar bana da ta ƙare.

Ana sa ran Kano Pillars za ta gabatar da Ogunmodede a hukumance cikin kwanaki masu zuwa, yayin da ƙungiyar ke ci gaba da shirye-shiryen tunkarar kakar wasan 2026/2027.

Rabilu Sanusi Bena
+ postsBio
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Yaya Toure Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Za’a Dakatar Da Wasa A Farkon Minti 10 Na Kowane Wasa A Kasar Argentina Saboda Girmama Messi

MASU ALAKA

Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia
Manyan Labarai

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato
Manyan Labarai

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Next Post
Mataimakin Shugaban Sin Ya Halarci Bikin Bude Taron Dandalin Tattauna Zaman Lafiya Na Duniya Karo Na 14 Tare Da Ba Da Jawabi

Mataimakin Shugaban Sin Ya Halarci Bikin Bude Taron Dandalin Tattauna Zaman Lafiya Na Duniya Karo Na 14 Tare Da Ba Da Jawabi

LABARAI MASU NASABA

Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.