Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya bayyana a yau Talata cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya samu tagomashi duk da matsin da ake fuskanta, kuma ya samu sabbin ci gaba a bana.
Da yake tattaunawa da shugabannin manyan hukumomin tattalin arziki na kasa da kasa a Beijing, Li Qiang ya ce suna da yakini da karfin cimma dukkan burikan kasar na samun ci gaban tattalin arziki da zaman takewa a bana.
Ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da fadada bude kofarta ga kasashen waje, kuma tana maraba da karin kamfanonin wajen su shigo kasar su ci gajiyar kasuwarta. (Mai fassara: FMM)
ADVERTISEMENT
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/