Kasar Sin na kara nuna tagomashinta a matsayin ginshikin ci gaban tattalin arzikin duniya ba na yanzu ba kawai, har ma da na gaba, yayin da manyan kamfanonin kasa da kasa ke ci gaba da karfafa zuba jarinsu na dogon zango a kasuwar kasar.
Duk da kalubalen rashin tabbas a tattalin arzikin duniya da kuma rikice-rikicen siyasa tsakanin kasashe da ake ta kara-kaina a ciki, manyan kamfanonin duniya na ci gaba da nuna cikakken kwarin gwiwa ga babbar damar da Sin ke da ita, musamman saboda girman kasuwarta, da saurin kirkire-kirkire, kakkarfan tsarin samar da kayayyaki, da kuma ci gaban masana’antu.Yanzu haka, kamfanoni irin su Apple da Nvidia na daga cikin manyan kamfanonin duniya da ke kallon Sin a matsayin muhimmiyar kasuwa ta fuskar samun bunkasa, da kirkire-kirkire, da kuma zuba jari.
Baya ga girman da kasuwar kasar Sin ke da shi, karuwar matsakaicin samun kudin shiga a kasar, na taka muhimmiyar rawa wajen samar da manyan damammaki a fannoni kamar fasaha, da kudi, da masana’antu, da kiwon lafiya, da sauran sassa, inda hakan yake kara bude sarari ga kamfanonin duniya masu neman fadada harkokinsu na dogon lokaci.
Kazalika, wani babban abin da ke kara jawo hankulan kamfanoni shi ne saurin bunkasar kirkire-kirkire a kasar Sin, ta yadda kamfanonin ke kallon kasar a matsayin wacce ke sahun gaba a fannoni kamar na kirkirarriyar basira, masana’antu masu amfani da fasahohin zamani, da tsarin biyan kudi na zamani, da fasahohin kiyaye lafiyar muhalli, wadanda suka kara fitar da kwarewar Sin wajen sarrafa sababbin fasahohi zuwa manyan harkokin kasuwanci.
Wasu jagororin ’yan kasuwa da suka rufa baya ga shugaban Amurka, Donald Trump a ziyarar da ya kawo kasar Sin ’yan makwannin baya, kamar shugaban kamfanin Mastercard, Michael Miebacha da shugaban majalisar ’yan kasuwar Sin da Amurka, Sean Stein, sun yi tsokaci kan ci gaban tattalin arzikin kasar Sin da ke samun sauye-sauye masu ma’ana, har ma musamman Miebacha ya ce, kamfaninsa ya mayar da hankali sosai kan kasuwar Sin domin cin gajiya na dogon zango tun daga shekarar 2024 da suka fara hada-hada a kasar.
A cewar Sean Stein kuwa, tattalin arzikin Sin ba wai kawai shi ne na biyu mafi girma a duniya ba, har ma ya kasance mai samun tagomashi a bangaren sabbin kirkire-kirkire, kana ya bukaci karfafa hadin gwiwa tsakanin Amurka da Sin domin samun ci gaban tattalin arzikinsu masu alaka da juna yadda ya kamata.
Himmatuwar da kasar Sin ke ci gaba da yi a bangaren nazari da samar da ci gaba ba kawai ga harkokin masana’antu ba har da na kyautata zamantakewar al’umma a bisa shirinta na ci gaban kasa na shekaru biyar-biyar, na ci gaba da karfafa matsayin kasar a matsayin babban ginshikin ci gaban tattalin arzikin duniya na gaba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














