ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto and Sulaiman
3 months ago
Dasuki

Mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, Hon. Abdussamad Dasuki, ya bukaci Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya gyara dangantaka da Jamhuriyar Nijar domin inganta tsaron iyakokin Arewa- maso- Yamma.

Dasuki wanda ke wakiltar mazabar Kebbe/Tambuwal a jihar Sakkwato ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da ya ziyarci hedikwatar jam’iyyar ADC ta jiha a inda ya jaddada muhimmancin kyautata hulda da makwabtan kasashe wajen magance matsalolin tsaro.

Dan majalisar ya bai wa gwamnoni shawara da su roki Shugaban Kasa da ya tabbatar an inganta dangantaka da makwabtan kasashe musamman Jamhuriyar Nijar.

ADVERTISEMENT

A cewarsa halin da dangantaka tsakanin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar ke ciki a yanzu ba abin jin dadi ba ne kuma ba alama ce mai kyau ga kalubalen sha’anin tsaro da ke addabar kasar nan ba. Kyakkyawar hulda tsakanin kasashen biyu na da matukar muhimmanci wajen dakile matsalolin tsaro da ke addabar yankunan kan iyaka.

Dan majalisar ya kuma bukaci gwamnati ta dauki karin matakai domin magance matsalar tsaro, ciki har da daukar ma’aikatan tsaron dazuka da kuma karawa hukumomin tsaro kudade.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Dasuki ya jaddada cewa samar da wadannan matakai za su taimaka matuka wajen dakile ayyukan ‘yan ta’adda da kuma inganta tsaro a yankunan karkara.

Haka kuma ya bukaci gwamnonin jihohi a fadin kasar nan da su tanadi isassun kudade domin aiwatar da shirin kafa ‘yansandan jihohi, yana mai cewa hakan na da muhimmanci wajen kusantar da tsaro ga al’umma da kuma magance matsalolin tsaro cikin gaggawa.

Dasuki
Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
+ posts Bio
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    2027:Cece-kuce Ta Barke Tsakanin Tinubu Da Atiku
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Yadda Rikici Ya Tsananta Tsakanin Dan Daba Da Malaman Addini A Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Dalilin Yawaitar Haduran Kwale-kwale A Yankin Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Atiku Ya Koka Kan Ƙaruwar Ta’addanci A Sakkwato
Dasuki
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.