ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

by CGTN Hausa and Sulaiman
3 months ago
Davos

An bude taron dandalin tattalin arzikin duniya na bazara wato DAVOS karo na 17 a birnin Dalian na lardin Liaoning dake arewa maso gabashin Sin a jiya Talata. Wakilai sama da 1700 daga kasashe da yankuna sama da 90 sun halarci taron, inda suka gudanar da tattaunawa kan “kafa cikakken tsari dangane da harkokin kirkire-kirkire a mabambantan bangarori” .

Taken wannan taron ya bayyana muhimman batun dake jawo hankalin shugabannin masana’antu a duniya, wato yadda sabbin fasahohi za su amfanar da mutane da yawa. “Wannan kuma shi ne matsalar da shugabannin kasashen duniya ke fuskanta gaba daya”, cewar daraktan zartarwa na dandalin Mirek Dusek. A wannan fanni, Sin ta riga ta taka rawar gani.

Bisa kididdigar kirkire-kirkire ta duniya da hukumar kiyaye hakkin mallakar ilmi ta duniya WIPO ta fitar, cikin manyan cibiyoyin kirkire-kirkire 10 dake sahun gaba a duniya, 5 sun kasance a Asiya, 3 daga cikinsu kuma a kasar Sin suke. Musamman ma a fannin AI, manhajar “Minds” na DAVOS ta ba da kididdiga cewa, kashi 60% na kamfanonin AI na duniya sun fito ne daga Asiya, kuma kusan rabinsu an kafa su ne a Sin. Sabbin kayayyakin kirkire-kirkire na iya samun miliyoyin masu amfani cikin sauri a kasar Sin, abun dake iya samar da bayanai masu dimbin yawa, matakin dake kara hanzarta bunkasar fasaha da kuma fadadar masana’antu.

ADVERTISEMENT

Wannan ya nuna cewa, Sin ba wai kawai mai shiga cikin kirkire-kirkire ta duniya ba ce, har ma muhimmin karfin ciyar da kafa cikakken tsarin amfani da kirkire-kirkire a mabambantan bangarori.

A yayin taron, ministan tattalin arzikin fasahar zamani da kirkire-kirkire na kasar Gabon Marc Alexandre Doumba ya yaba da fasaha da kirkire-kirkire da kwaskwarimar masana’antu na Sin sosai. Ya ce, muhimmiyar rawar Sin ita ce cimma nasarar kafa cikakken tsari bisa amfani da tushen masana’antunta mai karfi. Daga fasahar sadarwar intanet ta IoT dake cike da kuzari zuwa motocin lantarki masu ban mamaki, har zuwa manhajar kirkirarriyar basira ta DeepSeek mai karfin takara a duniya, wannan tsarin yana da ban sha’awa ga kasashe masu tasowa.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

DAVOS na bana ya fitar da wata alama cewa, Sin ba wai kawai muhimmiyar injin kirkire-kirkire ta duniya ba ce, har ma abokiyar hadin gwiwa ce mai aminci ga kasashe masu tasowa. Bugu da kari, manufar fadada bude kasuwarta da Sin ke aiwatarwa tana aza tubali mai albarka ga fitar da fasahar Sin zuwa kasashen waje, da hadin gwiwar kirkire-kirkire tsakanin kasashe masu tasowa da girka wannan tsari mai inganci a duniya. Saboda haka, Doumba ya mika gayyatar hadin gwiwa ga Sin, yana mai fatan kamfanonin Sin su shigo Gabon har da nahiyar Afirka, don su zuba jari da fasaha a fannoni kamar kiwon lafiya, makamashi da cibiyoyin bayanai da sauransu. Wannan ba wai fatan Gabon kadai ba ne, har ma fata ne na dukkan nahiyar Afirka.

Ba shakka, Sin ita ce damammaki ga Afirka, duba da yadda Doumba ya yaba da hanyar ci gaban Sin da ke ba da haske ga Afirka, da yadda kafafen yada labarai na kasashen Afirka da yawa suka yi kira ga Afirka da ta koyi kwarewar masana’antu daga Sin, kana da kuma yadda Sin ke aiwatar da manufar fadada bude kofarta ga ketare. Matakin dake bayyana ainihin ma’anar ka’idar “tattaunawa da ginawa da rarraba damammaki tare” da Sin ke gabatarwa Afirka.Taro na wannan karo ya zama karo na 9 da aka kira dandalin DAVOS a birnin Dalian.

DAVOS ba harkar Sin kadai ba ne, har ma ya zama wata dama ga duniya musamman kasashe masu tasowa, domin kara fahimtar Sin. Lokacin da wakilai sama da 1700 suka tattauna kan “kafa tsarin amfani da kirkire-kirkire a mabambantan bangarori” a wannan taron, abin da suke gani ba wai nasarorin fasaha na Sin kadai ba ne, har ma wata abokiyar hadin gwiwa dake rarraba damammaki bisa zarafin kirkire-kirkire.

Wannan ita ce alkawarin da Sin ke yi ga duniya, wato kasuwarta a bude take da nufin hadin gwiwa da bayyana tushen masana’antu mai karfi, tana kuma mayar da fa’idodin kirkire-kirkire zuwa damar ci gaban da ake rarrabawa ga duk fadin duniya, matakin da zai samar da kwanciyar hankali da tabbaci ga duniya mai rikici, musamman ma ga kasashe masu tasowa.(Marubuciya: MINA)

Davos
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Davos
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina Kasa

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 - Hakimin Makarfi

LABARAI MASU NASABA

Davos

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Davos

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.