Kasar Sin ta fitar da wani shiri na shekaru 5 domin bunkasa amfani da makamashi mai tsafta da rage fitar da hayakin carbon a bangaren masana’antu, inda ta tsara kai wa matsayin koli na fitar da hayakin carbon a shekarar 2030.
Ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar ce ta fitar da shirin wanda zai gudana tsakanin 2026 zuwa 2030, kuma manufar ita ce, kara amfani da makamashi mai tsafta a masana’antu da kara karfafa karfin takarar bangarorin samar da makamashi mai tsafta da na rage fitar da hayakin carbon.
Shirin ya tsara aiwatar da wasu ayyuka da suka hada da: aiwatar da shirye-shiryen kai wa matsayin koli wajen fitar da hayakin carbon daga masana’antu da fadada samar da kayayyakin samar da makamashi mai tsafta da karfafa kirkire-kirkiren fasahohi masu kare muhalli da inganta tsare-tsaren sake amfani da albarkatu a masana’antu. (Fa’iza Mustapha)














