Jam’iyyar NDC reshen Jihar Kano ta yi kira ga Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufai Sani Hanga da tsohon Gwamnan Kano tsohon sanatan Kano ta kudu Kabiru Ibrahim Gaya, da su janye daga shirin komawa jam’iyyar APC da ake zargin suna yi.
Shugaban NDC na Kano Hon. Hussaini Isah Mairiga, ya ce jam’iyyar za ta yi babban rashi idan manyan biyu suka fice. Ya bayyana cewa har yanzu ba su samu takardar murabus a hukumance daga gare su ba.
“Mu na kira gare su da su dakatar da wannan shiri. Su zo mu zauna mu tattauna. Duk matsalar da take akwai hanyar warware ta,” in ji Mairiga.
Ya ƙara da cewa duk da ganawar da Hanga da Gaya suka yi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin a Abuja, har yanzu NDC na ɗaukarsu a matsayin mambobinta.
Jam’iyyar ta ce za ta ci gaba da.barin ƙofar ta a buɗe ga dukkan ƴaƴanta domin ƙarfafa jam’iyyar a Kano.A kan wannnan dambarwa ta zaton ficewar Sanata Hanga daga NDC, ko a kwanakin baya ya yi taro da magoya bayansa domin suje su yanke hukunci abinda yakamata suyi zama a NDC ko sauya jam’iyya da a halin da ake ciki muƙarraban sanatan na cewa ADC da APC na zawarcinsu.














