ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, September 13, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasar Sin Ta Gabatar Da Takardar Bayani Game Da Inganta Tsarin Jagorancin Harkokin Duniya

by Sulaiman and CGTN Hausa
3 months ago
Sin

Da safiyar yau Laraba ne ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani mai taken “Kafa tsarin jagorancin harkokin duniya mai karin adalci: Akidun kasar Sin da shawararta da kuma matakanta”.

Takardar ta yi cikakken bayani a kan shawarar inganta tsarin jagorancin harkokin duniya da kasar Sin ta gabatar, musamman ta fannin kimiyya, da kuma ma’anarta ga duniya a wannan zamani da muke ciki, tare da bayyana matakan da kasar Sin ta dauka, da kuma nasarorin da ta cimma wajen sa hannu a inganta tsarin jagorancin harkokin duniya. Har ila yau, takardar ta yi kira ga sassan kasa da kasa da su aiwatar da shawarar inganta tsarin jagorancin harkokin duniya, don kafa tsari mai karin adalci.

A gun taron manema labarai da aka shirya dangane da takardar, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne ministan harkokin wajen kasar, Mr. Wang Yi, ya amsa tambayar da aka yi masa dangane da yadda ake komawa cikin yanayin yadda masu karfi ke cin zalin marasa karfi, tare da raunata karfin fada a ji na MDD, inda ya bayyana matsayin kasar Sin na kiyaye cudanyar bangarori daban daban, da goyon bayan rawar da MDD ke takawa. Wang Yi ya ce, ba wai MDD ba ta da muhimmanci ba ne, sai dai ba a mutunta da kiyaye ta yadda ya kamata.

ADVERTISEMENT

A matsayinta na kasa ta farko da ta sanya hannu kan kundin tsarin dokokin MDD, kasar Sin tana son kiyaye karfin fada a ji na MDD ta hanyar aiwatar da shawarar inganta jagorancin harkokin duniya, kuma tana son hada kai da sassan kasa da kasa, a kokarin farfado da MDD da kuma kara bunkasa ta.

A yayin taron, Wang Yi ya yi bayani game da fannoni guda 4 da kasar Sin za ta dukufa domin inganta tsarin jagorancin harkokin duniya.

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi

Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT

Da farko, ya ce za a farfado da ra’ayin raya yankuna gaba daya cikin hadin gwiwa. A bana, kasar Sin za ta gudanar da taron ganawar shugabannin kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin yankin Asiya da Pacifik ta APEC, inda za a samar da sabbin damammaki ga bunkasuwar kasashen dake yankin Asiya da Pacifik, har ma da kasashen duniya baki daya. Na biyu kuma, za a karfafa aikin gudanar da sabbin ayyuka. Na uku kuma, za a inganta aikin gina dandalolin jagorancin harkokin duniya. Kasar Sin ta yi maraba da sassan kasa da kasa, da su shiga kotun shiga tsakani ta kasa da kasa da kasar Sin ta yi kira a kafa, domin ba da gudummawa wajen warware sabanin dake tsakanin kasashen duniya cikin zaman lafiya. Na hudu kuma, ana sa ran kasashen duniya za su cimma matsayi daya kan tsarin jagorancin harkokin duniya.

A bana, kasar Sin za ta kira taron dandalin tattauna tsarin jagorancin harkokin duniya a sabon yankin Xiong’an karo na farko, inda za ta gayyaci wakilan bangarori daban daban daga kasashen duniya, domin tattauna yadda za a daidaita, da kuma kyautata tsarin jagorancin harkokin duniya.

Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Hafsat Bakari Ta Sake Dawo Da Sarƙaƙƙen Al’amari
  • Sulaiman
    Zan Yi Amfani Da Dukiyata Wajen Samun Nasarar Gwamnan Jihar Kano A 2027 – Amb Adesuwa
  • Sulaiman
    Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi
  • Sulaiman
    Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT
Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Masu Kera Motoci Na Kasar Sin Sun Lashe Lambobin Yabo Da Dama A Bikin Nune-nunen Motoci Na Turin
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

MASU ALAKA

Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi
Daga Birnin Sin

Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi

September 12, 2026
Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT
Daga Birnin Sin

Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT

September 12, 2026
Masu Kera Motoci Na Kasar Sin Sun Lashe Lambobin Yabo Da Dama A Bikin Nune-nunen Motoci Na Turin
Daga Birnin Sin

Masu Kera Motoci Na Kasar Sin Sun Lashe Lambobin Yabo Da Dama A Bikin Nune-nunen Motoci Na Turin

September 12, 2026
Next Post
Sin Na Gaggauta Kafa Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI Ta Kasa Da Kasa

Sin Na Gaggauta Kafa Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI Ta Kasa Da Kasa

LABARAI MASU NASABA

Hafsat Bakari Ta Sake Dawo Da Sarƙaƙƙen Al’amari

Hafsat Bakari Ta Sake Dawo Da Sarƙaƙƙen Al’amari

September 13, 2026
Zan Yi Amfani Da Dukiyata Wajen Samun Nasarar Gwamnan Jihar Kano A 2027 – Amb Adesuwa

Zan Yi Amfani Da Dukiyata Wajen Samun Nasarar Gwamnan Jihar Kano A 2027 – Amb Adesuwa

September 13, 2026
Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi

Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi

September 12, 2026
Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT

Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT

September 12, 2026
jam'iyyu

An Buƙaci Ƴan Takara Su Sanya Tsare-tsaren Yaƙi Da Ɗumamar Yanayi A Jaddawalin Kamfen Ɗinsu

September 12, 2026
Masu Kera Motoci Na Kasar Sin Sun Lashe Lambobin Yabo Da Dama A Bikin Nune-nunen Motoci Na Turin

Masu Kera Motoci Na Kasar Sin Sun Lashe Lambobin Yabo Da Dama A Bikin Nune-nunen Motoci Na Turin

September 12, 2026
Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Amince Da Tsawaita Takunkuman Sudan Na Gajeren Lokaci

Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Amince Da Tsawaita Takunkuman Sudan Na Gajeren Lokaci

September 12, 2026
Xi Ya Gana Da Modi A New Delhi

Xi Ya Gana Da Modi A New Delhi

September 12, 2026
2027: Masana Sun Yi Gargaɗi Game Da Bangar Siyasa Da Kalaman Ɓatanci

2027: Masana Sun Yi Gargaɗi Game Da Bangar Siyasa Da Kalaman Ɓatanci

September 12, 2026
Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa

Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa

September 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.