ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Da Atiku Da Obi Na Ci Gaba Da Zafafa Neman Kuri’un Arewacin Nijeriya

by Yusuf Shuaibu
2 months ago
Atiku

Ana gwada kwanji a tsakanini ‘yan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu da Atiku Abubakar da Peter Obi domin samun kuri’u masu rinjaye a yankin Arewacin Nijeriya a lokacin zaben 2027.

A kan wannan ne cacar baki ta kaure a tsakanin tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, da tsohon gwamnan Jihar Borno, Ali Modu Sheriff, na kokarin samun goyon baya a yankin Arewacin Nijeriya.

Sheriff, yayin magana kan sauye-sauyen da ke gabatowa kafin zabin shugaban kasa a wata hira a shirin siyasa ta yau na gidan talabijin na Channels TB, ya ce masu kada kuri’a na Arewa ba za su taba goyon bayan Peter Obi ba. Kwankwaso ya yi watsa da ikirarin, yana jaddada cewa babu wani mutum da ke da hurumin magana a madadin Arewa.

ADVERTISEMENT

Cacar bakin ya zama muhawara a talabijin da sharhi a jaridu da kuma dogon tattaunawa a cikin harkokin siyasa.

Amma masu nazari kan harkokin siyasa a Nijeriya sun gano cewa cacar bakin ba wai game da Peter Obi ko wani dan takara na shugaban kasa ba. Abin yana da zurfi fiye da haka. Wanda, bayan Muhammadu Buhari, mutum zai iya fahimtar cewa ko jan ragamar zuciyar siyasa a Arewacin Nijeriya yana da sauki? Wannan tambaya ce da yanzu take tsakiyar duk wani lissafin zaben 2027. mai mahimmanci.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

Tsawon shekaru masu yawa, ‘yan siyasa sun na magana game da Arewa kamar dai idan dan sayasa ya samu nasara a yanki shi ne zai zama shugaban kasa a duk wani zabe da zai gudana.

Masana harkokin siyasa a Nijeriya sun tabbatar da cewa yankin Arewa yana da matukar tasiyasa a duk wani zabe a Nijeriya.

Zaben 2023, ya nuna karara cewa Arewa tana da tasiri a zaben Nijeriya. Maimakon jama’a su hadu a bayan wani dan takara na Arewa mai rinjaye, masu kada kuri’a sun rarrayabu a jam’iyyu daban-daban na siyasa. Tinubu ya samu babban goyon baya kuma a karshe ya tabbatar da samun shugabancin kasa. Atiku Abubakar ya yi tasiri a sassan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma. Kwankwaso ya yi nasara a Kano a jam’iyyar NNPP. Peter Obi ya samu nasara a wasu sassan Arewa ta tsakira.

Wannan sauyi ya sa siyasar Arewa ta zama mai bude kofa ga duk dan takarar da ya cancanta.

Yayin da shekarar 2027 ke karatowa, dukkan manyan jam’iyyun siyasa na ganin cewa Arewan Nijeriya har yanzu ita ce wuri mafi muhimmanci na fafatawa.

APC na ganin kasancewa tana da mulki, za ta samu damar kara fadada tasirinta a yanki wanda hakan zai sa samu nasara a zaben 2027. Yayin da ‘yan adawa na cewa kwancin tattalin arziki da rashin tsaro za su haifar da yanayin sauyin siyasa a yankin.

Shin Arewacin Nijeriya ya shiga wani sabon zamani na siyasa ne, wanda babu wani dan siyasa guda daya da zai iya da’awar mallakar yankin. Lokaci ne kawai zai tabbatar da haka.

Atiku
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
Sin Za Ta Inganta Kaddamar Da Aikin Kungiyar Hadin Gwiwar AI Ta Duniya Da Wuri

Sin Za Ta Inganta Kaddamar Da Aikin Kungiyar Hadin Gwiwar AI Ta Duniya Da Wuri

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.