Sarkin Musulmi Attahiru (1)
Turawan mulkin-mallaka sun kashe Sarkin Musulmi Attahiru ne a garin Mbormi da ke jihar Gombe a yanzu Sarkin Musulmi Attahiru na daga cikin mutane waɗanda da suka nuna rashin amincewarsu ba tare da wani yin rufa- rufa ba ga Turawan mulkin mallaka.
Sarki Muhammadu Attahiru, shi ne Sultan wato Sarkin Musulmi na 12 kuma na ƙarshe kamar yadda sunayen Sarakunan y su ke tun daga abin kuma ya fara ne tun daga mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodio, kafin Turawan mulkin mallaka su zo su ƙwace iko daga Daular.
Lokacin mulkinsa ya yi gwagwagwa da turjiya da zuwan suTurawan mulkin mallaka waɗ
anda suka fara shiga Arewacin Nijeriya a shekarar 1890
Dakta Abdullahi ya ce (Sultan) Sarkin Musulmi Attahiru ya jagoranci mayaƙansa ne suka nuna rashin yin mubayi’a wa Turawan, lamarin da abin yasa har ya kai ga yin yaƙi har Turawan suka fitar da shi daga ƙasarsa, kafin daga baya suka kashe shi a wani gari da ke cikin jihar Gombe a yanzu.
Muhammadu Attahiru II
Shi ma Sarkin Musulmi Muhammadu Attaihiru wanda ya hau kan karagar Sarautar daga baya, bai ɓata wani lokaci ba wajen yin turjiyar shi wa Turawan, kamar yadda Dakta Abdullahi ya bayyana.
Muhammadu Attahiru, ya yi mulkin ne daga 1903 zuwa 1915.
Turawan mulkin mallakar sun naɗa shi ne naɗa da wata manufa ta samun yin iko da ita Daular, to amma sai ya ƙi ba da kai bori ya hau, domin kuwa ai bai manta da abin da ya faru da mahaifinsa ba’, cewar shi masanin tarihin.
Ko da shi ma ya nuna alamun ba zai amince da umarninsu ba, bare ma ya yi amfani da shi, shi ma daga ƙarshe dai shi ma ai sai da suka yaƙe shi.
Sarkin Kano Alu (Babba)
Dakta Abdullahi ya ce Sarkin Kano Alu Babba wanda ya mulki Kanon daga shekarar 1894 zuwa 1903 ya kasance cikin fitattu kuma mashahuran Sarakunan Arewacin NIjeriya da suka nuna turjiyarsu, da bijirewarsu ga su Turawan mulkin mallakar.
Wannan tarihin mun samo masku shi ne daga shafin Facebook na sashen Hausa BBC













