ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Manoma Sama Da 20 A Zamfara – Amnesty International

by Sadiq
2 months ago

Aƙalla manoma sama da 20 ne suka rasa rayukansu bayan da ‘yan bindiga suka kai hari wasu ƙauyuka da ke Jihar Zamfara a ranar Laraba, kamar yadda ƙungiyar Amnesty International ta bayyana.

Rahotanni sun ce manoman na komawa daga gonakinsu ne lokacin da maharan suka kai musu hari.

Wani da ya tsallake rijiya da baya daga harin ya shaida wa BBC Hausa, cewa maharan sun zo ne da babura masu yawa, suka kewaye mutanen, sannan suka riƙa bin su suna harbewa.

ADVERTISEMENT

Ya ce, duk wanda ya yi ƙoƙarin guduwa, ‘yan bindigar kan bi shi da babur, su harbe shi, sannan su tattake shi.

Haka kuma sun tattara dabbobin mutanen sannan suka tafi da su.

LABARAI MASU NASABA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

Majiyar ta ce maharan sun kai kimanin 100, kuma sun fito ne daga yankin Jangebe.

Ya ƙara da cewa ya ga gawarwakin mutane sama da 20 da idonsa.

An kai harin ne a ƙauyukan Sauna, Tudun Namale, Tsangaya, Mashekari da kuma Unguwar Shanu.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook, Amnesty International ta ce mutane 24 ne aka kashe, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Ƙungiyar ta ce hare-haren na nuna cewa matakan da ake ɗauka wajen magance matsalar tsaro a Zamfara ba su samar da sakamakon da ake buƙata ba.

Amnesty ta kuma ce ‘yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare ƙauyukan jihar, inda a wasu lokuta suke sanar da mazauna ƙauyukan kafin su kai hari tare da neman haraji ko kuɗin fansa.

Jihar Zamfara da wasu jihohin Arewa maso Yamma na fama da hare-haren ‘yan bindiga sama da shekara 10, inda ake kashe mutane, sace su domin neman kuɗin fansa, tare da ƙone gidaje da lalata dukiyoyi.

Duk da cewa hukumomin tsaro na cewa suna ɗaukar matakan shawo kan matsalar, hare-haren na ci gaba da aukuwa a yankunan da abin ya shafa.

MASU ALAKA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro
Manyan Labarai

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 11, 2026
Manyan Labarai

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
Manyan Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Next Post
Wang Yi Ya Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio

Wang Yi Ya Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026
Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

September 11, 2026
Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

September 11, 2026
Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

September 11, 2026
Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe

Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen

September 11, 2026
Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC

2027: A Karon Farko INEC Za Ta Ƙaddamar Da Na’urar Bibiyar Zaɓen Nijeriya

September 11, 2026
Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

September 11, 2026
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026  Mrs Zubaida Umar

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

September 11, 2026
Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.